Kyauta daga Allah: An tabbatar da gaskiyar labarin matar da ta haifi jarirai 10
- Bayan karyata labarin matar da ta haifi jarirai 10 a lokaci daya, gwamnati ta tabbatar da labarin
- Gwamnatin kasar ta bayyana cewa, ta samu isa ga dangin da suka haifi jariran, inda ake tallafa musu
- Mutane da dama sun shiga ta'ajibin lamarin wanda ya kasance bako a samu mutum da haihuwar jarirai 10
Wata sanarwa da wata mai magana da yawun gwamnati, Phumla Williams ta yi kwanan nan, ta bayyana cewa gwamnati ba ta da wata shaida da ke nuna cewa wata mata Gauteng mai suna Gosiame Thamara Sithole ta haifi jarirai 10 a lokaci guda.
"Gwamnati ta kasa tantance sahihancin waccar haihuwar a cibiyoyinmu," in ji wani bangare na sanarwar da Williams ta fitar.
Tun da farko an samu shakku game da labarin haihuwar mai ban mamaki na wata matar da aka ce ta haifi jarirai 10 a kasar Afrika ta Kudu.
KU KARANTA: Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna
"Ofishina da Sashenmu na Ci Gaban Jama'a suna ta neman dangin da ake cewa sun haifi yara 10 a yau. A bayyane, sun kasance daga Tembisa kuma muna son taimakawa a matsayin birni.
"Shin @IOL na iya ba da wasu bayanai game da wannan labarin? Ko kuwa kafofin watsa labarai na yau da kullun sun koma masana'antar labarai ta bogi ne?"
In ji wani rubutu daga Mzwandile Masina, Shugaban yankin ANC Ekurhuleni.
Da yawa daga cikin mazauna sun nuna rudaninsu game da lamarin. Yayin da da yawa daga cikinsu suka fara tambayar labarin haihuwar mai ban mamaki, wasu kuma sun ba da dan karamin bayanin da suke da shi:
@ Timzone5 ya ce:
"Ina kwana Shugaba na. Maigidan wanda ya haifi jarirai 10 a Tembisa abokina ne kuma ba labarin karya bane, zan iya shirya ganawa da shi."
@ tendani1yahooc1 ya ce:
"Wannan labarin da kura a cikinsa. Me ya sa babu asibiti da ya fito ya ba da sanarwar wannan abin al'ajabi? Ina nufin, asibitoci ba za su taba rasa damar yin kanun labarai ba. Babu wani tashar talabijin da ke daukar labarin. Akwai alamar tambaya anan."
Sa’o’i kadan bayan haka, wani jami’in gwamnati, Mzwandile Masina, ya ce an gano dangin da suka haifi jariran.
Ta ce:
"Mun gano dangin kuma an sanar da mu cewa jariran suna cikin koshin lafiya. Za mu bada bayanin ga gwamnati, na san mun kasance abin dariya a jiya lokacin da gwamnati ke neman dangin.
"Wasu daga cikin 'yan uwanmu na gida suna taimaka wa wannan dangin. Don haka ya yi kyau..."
KU KARANTA: Ku taimaka ku ceci Najeriya: NCF ta roki Gowon, sauran tsoffin shugabanni
A wani labarin, Wata mata yar kasar Mali ta haifi yan tara a Morocco a ranar Talata kuma dukkan jariran tara 'lafiyarsu kalau', a cewar gwamnatin kasarta duk da cewa mahukunta a Morocco ba su tabbatar da hakan ba, The Punch ta ruwaito.
Gwamnatin kasar Mali ta kai Halima Cisse mai shekaru 25 daga yankin arewacin kasar zuwa Morocco domin samun ingantaccen kulawa a ranar 30 ga watan Maris. Da farko ana tunanin yan bakwai za ta haifa.
Yana da wahala samun mata da ke haihuwan yan bakwai cikin koshin lafiya - balantana yan tara.
Asali: Legit.ng