Kyauta Daga Allah: Wata Mata Ta Haifi Ƴan Tara a Morocco

Kyauta Daga Allah: Wata Mata Ta Haifi Ƴan Tara a Morocco

- Wata mata yar kasar Mali mai suna Halima Cisse yar shekara 25 ta haifi yan tara a kasar Morocco

- Ministan Lafiya na Mali, Fanta Siby ta ce likitocin da suka raka Cisse Morocco sun tabbatar mata da hakan

- Siby ta mika sakon taya murna ga likitocin Mali da Morocco bisa nasarar da suka samu na tiyatar haihuwan

Wata mata yar kasar Mali ta haifi yan tara a Morocco a ranar Talata kuma dukkan jariran tara 'lafiyarsu kalau', a cewar gwamnatin kasarta duk da cewa mahukunta a Morocco ba su tabbatar da hakan ba, The Punch ta ruwaito.

Gwamnatin kasar Mali ta kai Halima Cisse mai shekaru 25 daga yankin arewacin kasar zuwa Morocco domin samun ingantaccen kulawa a ranar 30 ga watan Maris. Da farko ana tunanin yan bakwai za ta haifa.

Kyauta Daga Allah: Wata Ta Haifi 'Yan Tara a Kasar Mali
Kyauta Daga Allah: Wata Ta Haifi 'Yan Tara a Kasar Mali. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abun Al’ajabi: Wata Mata Da Bata San Tana Ɗauke Da Juna Biyu Ba Ta Haihu a Jirgin Sama

Yana da wahala samun mata da ke haihuwan yan bakwai cikin koshin lafiya - balantana yan tara.

Kakakin ministan Lafiya na Morocco Rachid Koudhari ya ce ba su da masaniya kan haihuwar yan tara a asibitin kasarsu.

Amma ma'aikatar lafiya na kasar Mali cikin wata sanarwa ta ce Cisse ta haifi mata biyar da maza hudu ta hanyar yi mata tiyata.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo

"Mahaifiyar da yaran dukkansu lafiyarsu kalau a halin yanzu," a cewar ministan lafiya Fanta Siby kamar yadda ya shaidawa AFB, ta kara da cewa likitocin Mali da suka yi wa Cisse rakiya zuwa Morocco suka tabbatar mata hakan.

Za su dawo cikin yan makonni, ta kara da cewa.

Likitoci suna damuwa kan halin da Cisse da jariranta ke ciki a cewar jaridun kasar.

Ma'aikatar lafiya na Mali cikin sanarwar da ta fitar da ce gwajin ultrasound da aka yi a Mali da Morocco ya nuna cewa juna biyun da Cisse ke dauke da su yan bakwai ne.

Siby ta mika sakon taya murna ga likitocin Mali da Morocco kan nasarar da suka samu tare da kwarewarsu wurin aiki.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel