Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Garkuwa Sun Sace Malamar Makaranta a Abuja

Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Garkuwa Sun Sace Malamar Makaranta a Abuja

- Masu garkuwa da mutane sun kutsa gidan wata malamar makaranta a Kuje sun sace ta

- Wani daga cikin yan uwan malaman ya ce masu garkuwar sun nemi a biya N10m kudin fansa

- Sakataren kungiyar malaman makaranta, NUT, reshen karamar hukumar Kuje, Nathan Magaji ya tabbatar da afkuwar lamarin

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace malama a makarantar sakandare a gwamnati da ke Kuje, babban birnin tarayya, Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun ce an sace matar mai suna Mrsa Daramola Onyeaka Matina ne a cikin gidan ta da ke garin Shadadi da ke karamar hukumar Kuje.

Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Garkuwa Sun Sace Malamar Makaranta a Abuja
Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Garkuwa Sun Sace Malamar Makaranta a Abuja
Asali: Original

Wani dan uwanta da ya nemi a boye sunansa ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Majalisa Za Ta Tantace Hadimar Buhari Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Kwamishinoni a INEC

Ya ce masu garkuwar dauke da muggan makamai sun kutsa gidan ta misalin karfe 12.34 na dare.

"Ta kofan baya suka shiga gidan. Sun yi amfani da babban guduma da gatari wurin lalata kofar, yayin da wasu suka tsaya a waje suka zagaye gidan. Daga bisani suka tafi da ita," in ji shi.

Ya ce yan uwan sun yi magana da masu garkuwar kuma sun nemi a biya naira miliyan 10 kudin fansa.

"An yi magana da wadanda suka sace ta a yammacin ranar Talata, suna neman a biya su naira miliyan 10 duk da cewa ana cigaba da tattaunawa," in ji shi.

Sakataren kungiyar malaman makaranta, NUT, reshen Kuje, Kwamared Shamaki Nathan Magaji ya tabbatar da sace malaman a hirar wayar tarho da aka yi da shi.

KU KARANTA: Hotunan Dakarun NSCDC Mata Zalla Da Ya Ɗauki Hankulan Mutane a Dandalin Sada Zumunta

Ya ce sun sanar da kungiyar a matakin jiha.

Da aka tuntube ta, mai magana da yawun yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta bukaci wakilin majiyar Legit.ng ya tura mata sakon kar ta kwana amma bata amsa ba a lokacin hada wannan rahoton.

A wani rahoton daban kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.

Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164