Da Ɗuminsa: FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa

Da Ɗuminsa: FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa

- Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan matakin da ake na ɗaukar ma'aikata a shirin N-Power

- Ministan Ma'aikayar jin ƙai da walwala, Sadiya Farouq, ita ce tayi jawabi dangane da shirin yau a Abuja

- Tace a halin yanzun an zaɓi mutum 550,000 waɗanda suka tsallake matakin tantancewa

Ma'aikatar jin ƙai da walwala ta bayyana cewa aƙalla mutum 550,000 ne suka tsallake matakin tantancewa daga cikin mutum 1.8 miliyan da suka nemi gurbin aiki a shirin npower.

KARANTA ANAN: Sunayen Wasu Makusantan Shugaba Buhari da Suka Bijire Wa Umarninsa Na Hana Amfani da Twitter

Hajiya Sadiya Farouq, ministar ma'aikatar jin kai da walwala, ita ce ta bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Farouq tace a watan Maris, ma'aikatarta ta ƙaddamar da shirn NASIMS domin ma'aikatan npower da zata ɗauka a rukunin C, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan Ɗaukar Ma’aikatan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa
FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan Ɗaukar Ma’aikatan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa Hoto: @sadiya.farouq
Asali: Instagram

Ta ƙara da cewa an nemi waɗanda suka nemi shiga tsarin da su je shafin yanar gizo na NASIMS su sake cike bayanan su, sannan su amsa wasu tambayoyin gwaji.

Ministan tace: "Mun sake tantacewa, a yanzun mun zaɓi mutum 550,000 waɗanda suka cancanta suje matakin ƙarshe, inda zamu zaɓi mutum 500,000 da zasu yi aiki a sashin farko na rukunin C."

"Wanan shine rukunin C 1, sashin na biyu na rukunin zai biyo baya inda zamu sake ɗaukar mutum 500,000 domin cika umarnin shugaban ƙasa na ɗaukar miliyan ɗaya."

KARANTA ANAN: Wani Kwamishina Ya Rasa Muƙaminsa Saboda Yaƙi Bin Gwamna Zuwa APC

Ministan ta ƙara da cewa an tuntuɓi mutum 550,000 ɗin da aka zaɓa ta hanyar e-mail dinsu, kuma an umarce su da du ziyarci NASIMS domin ɗaukar hoton yatsunsu.

A wani labarin kuma Manyan Dalililai 5 da Suka Tabbatar da Mutuwar Shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau

A makonni biyu da suka gabata rahoton mutuwar shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau ya karaɗe kafafen watsa labarai.

Bayan bayyanar rahoton mutuwar tasa, wasu na ganin ai wannan ba shine karo na farko da ake cewa ya mutu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel