Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa ta farko da wasu abubuwa 5

Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa ta farko da wasu abubuwa 5

Kowa ya san Aisha Buhari a matsayin matar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma ba kowa ya san cewa akwai wata mace da ake kira Safinatu Buhari ba.

Ta kasance malamar makaranta kuma marigayiya matar shugaban kasa wacce ta kasance a matsayin matar shugaban kasar Najeriya lokacin da mijinta ya rike mukamin shugaban kasa tsakanin 1983 da 1985.

Legit.ng ta kawo muku tsoffin hotunan Safinatu da abubuwa shida game da ita.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: 'Yan kasuwar Arewa suna barazanar yanke hanyar samar da abinci a kasa baki daya

Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa da farko da wasu abubuwa 5
Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa da farko da wasu abubuwa 5 Hoto: Nairaland
Asali: UGC

1. Haihuwa da kuma aiki

An haifi Safinatu Buhari a shekarar 1952 a garin Jos, jihar Plateau. Iyayenta sune Alhaji Yusuf Mani da Hajiya Hadizatu Mani. Ta kasance malama da aka horar wacce ta samu takardar shedar kammala karatinta na 2 a Kwalejin malamai mata (WTC), Katsina, a shekarar 1971, rahoton Fulani News Media.

Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa da farko da wasu abubuwa 5
Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa da farko da wasu abubuwa 5 Hoto: Herald
Asali: UGC

2. Ta hadu da Buhari lokacin tana yar shekara 14

Buhari da Safinatu sun hadu da juna yayin da ta ke da shekaru 14 a duniya.

A lokacin haduwarsu, Buhari wanda yake cikin rundunar Sojojin Najeriya ya raka abokinsa, Marigayi Janar Shehu Musa Yar’adua, don ganin mahaifin Safinatu.

3. Aure tsakanin su biyun

Yakin basasar Najeriya ya ƙare a 1970 kuma Muhammadu Buhari da Safinatu sun yi aure a cikin Disamba 1971 lokacin da Safinatu ke da shekaru 18.

4. Sun kasance da yara huɗu tare

Safinatu da Buhari suna da yara huɗu tare, dukansu mata.

Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa da farko da wasu abubuwa 5
Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa da farko da wasu abubuwa 5 Hoto: Flatimes
Asali: UGC

5. Aurenta da Buhari ya mutu

A cewar City People, lokacin da aka saki Buhari daga tsare, ya kawo karshen aurensa da Safinatu. Ba a bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar ba amma mutane da yawa sun yi amannar cewa saboda Safinatu ta ki bin umarnin mijinta ne na kau da kai daga dangin Babangida.

KU KARANTA KUMA: Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki

Ibrahim Babaginda ya hambarar da gwamnatin Buhari a wani juyin mulki ya sa shi a tsare. Yayin da ake tsare da shi, Buhari ya gargadi Safinatu da kada ta yi wata alaka da dangin mai tsaron nasa.

Safinatu ta yi ma'amala da Babangida ta wani bangare don taimaka mata wajen fuskantar rayuwa, da kuma yin amfani da damar don sakin mijinta.

6. An gano tana dauke da ciwon suga

Safinatu ta kamu da ciwon suga ne a shekarar 1998. Ta rayu da cutar tsawon shekaru takwas kafin ta yi ajalinta a ranar 14 ga Janairun 2006.

Waiwaye: Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace ya haifar da cece kuce

A wani labarin, wani tsohon hoto na Shugaba Buhari yana more rayuwa lokacin da yake matashi ya haifar da zazzafan martani a shafukan sada zumunta.

Wani ma’abocin amfani da Facebook mai suna Ayo Ojeniyi ya dimauta yanar gizo da wani hoto wanda ba kasafai ake gani ba na Shugaba Buhari yayin da wani saurayi yake rawa da wata farar mace ba takalmi.

Buhari ya kasance dauke da murmushi yayin da suke rawa inda sauran matan da ke wurin suke kallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel