Dakatar da Twitter salo ne na kawar da hankalin 'yan kasa daga gazawar FG, Ortom

Dakatar da Twitter salo ne na kawar da hankalin 'yan kasa daga gazawar FG, Ortom

- Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai yace dakatar da Twitter hanya ce da gwamnatin tarayya ta bi na rufe gazawarta

- Kamar yadda ya bayyana a wata wallafa da yayi a Twitter ranar Talata, yace FG ta rufe gazawarta ne a fannin tsaro

- Ya kara da cewa dakatar da twitter take hakkin dan Adam ne tare da takurawa da toshe kafafen sada zumunta

Samuel Ortom, gwamnan jihar Binuwai, ya ce dakatar da Twitter hanya ce ta kawar da hankulan 'yan Najeriya wacce gwamnatin tarayya ta samo domin rufe gazawarta a fannin shawo kan rashin tsaro.

A wata wallafa da yayi a Twitter a ranar Talata, Ortom yace dakatarwan an yi ta ba bisa ka'ida ba inda ya kwatanta lamarin da takura tare da danne hakkin 'yan Najeriya.

Gwamnan jihar Binuwai din ya kara da cewa wannan abu da gwamnati tayi wata hanya ce ta toshe kafafen sada zumuntar zamani, The Cable ta ruwaito.

"Dakatar da Twitter ba wai karya doka kadai aka yi ba, amma shawara ce mara kyau wacce gwamnatin tarayya ta runguma domin kawar da hankulan 'yan Najeriya kan matsalar tsaro a kasar nan," ya wallafa a Twitter.

KU KARANTA: Gwamna Mai Mala Buni ya magantu kan rade-radin zai sauka daga shugabancin Yobe

Dakatar da Twitter salon FG ne na kawar da hankalinmu daga rashin tsaro, Ortom
Dakatar da Twitter salon FG ne na kawar da hankalinmu daga rashin tsaro, Ortom. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Kafin ku koma Ghana saboda Twitter, buhun shinkafarsu N48,000 ne, Hadimin Aisha Buhari

"Wannan daidai yake da danne hakkin dan Adam tare da toshe kafafen sada zumunta."

Wallafar Ortom tana zuwa ne bayan kwana daya da Enoch Adeboye, shugaban Redeemed Christian Church of God, ya bayyana sukarsa a kan hukuncin gwamnatin.

A makon da ya gabata, Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya sanar da dakatar da Twitter a kasar nan.

Wannan cigaban na zuwa ne bayan da Twitter ta cire wallafar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Duk da kamfanonin sadarwa sun datse hanyoyin shiga Twitter bayan umarnin gwamnatin, 'yan Najeriya masu tarin yawa sun koma kafar ta hanyar amfani da VPN.

A wani labari na daban, jami'an kamfanin jirgin sama na Air Peace sun bankado wani yunkurin sace jarirai biyu a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mutum tare da wata mata ne suka kusa tafiya da yaran a ranar 7 ga watan Yunin 2021 a filin jirgin sama dake Legas.

An gano cewa matar da namjin na kan hanyarsu ne ta zuwa Asaba yayin da aka tsaresu domin duba kayansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng