Gwamna Mai Mala Buni ya magantu kan rade-radin zai sauka daga shugabancin Yobe

Gwamna Mai Mala Buni ya magantu kan rade-radin zai sauka daga shugabancin Yobe

- Wasu mambobin APC suna ikirarin cewa Gwamna Buni na jihar Yobe yana shirin murabus daga kujerar gwamnan domin ya samu damar shugabantar APC

- Mambobin jam'iyyar wanda ba a bayyana sunansu ba, sun ce wannan shirin da Buni ke yi na daga cikin dalilinsa na kawo tsaiko a zaben jam'iyyar

- Amma kuma Gwamna Buni, ta bakin hadiminsa na fannin yada labarai, ya musanta cewa zai yi murabus inda ya kwatanta hakan da 'bakar karya'

Akwai hasashe tare da rade-radin cewa Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, yana shirin yin murabus daga shugabancin jihar Yobe domin ya samu damar shugabantar jam'iyyar APC, ThisDay ta ruwaito.

Gwamna Buni wanda shine shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya zai kammala wa'adin shugabancin jihar Yobe a karo na biyu a 2023.

KU KARANTA: Sunaye: Bayan nadin sabon COAS, rundunar soji ta yi wa manyan sojoji 29 ritayar dole

Gwamna Mai Mala Buni ya magantu kan rade-radin zai sauka daga shugabancin Yobe
Gwamna Mai Mala Buni ya magantu kan rade-radin zai sauka daga shugabancin Yobe. Hoto dag tribuneonlineng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Dan sanda ya sheka lahira yayin da 'yan bindiga suka kashe manoma 41 a Zamfara

Jaridar ta kara da cewa ana tsammanin burin Gwamna Buni ne yasa aka dakatar da sanar da ranar zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.

Amma kuma an ruwaito cewa Gwamna Buni ya musanta wannan zargin na shirin murabus daga kujerar gwamna domin zama shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Hadimin gwamnan na fannin yada labarai, Mamman Mohammed, ya ce tuni gwamnan yana da nauyi a kansa don haka baya neman wani.

A kalamansa: "Bakar karya ce, shiryayyen zance ne. Gwamnan yana da aikin da yake kuma baya bukatar wani aiki."

Mohammed yace aikin da aka baiwa Gwamna Buni shine gyaran APC, shirya zaben shugabanni da mika ragamar shugabancin jam'iyyar ga sabbin shugabanni.

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun sake kashe manoma 41 a kauyukan Tofa da Samawa na karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin wanda yace sunansa Malam Balarabe, ya sanar da The PUNCH cewa 'yan bindigan sun kutsa yankin yayin da manoman ke gonakinsu suna shuka, wasu kuma suna gyaran gona.

"Kwatsam suka bayyana sannan suka dinga harbin manoman inda suka kashe da yawa daga ciki," Balarabe ya jaddada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng