Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya bankado yunkurin safarar jarirai 2

Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya bankado yunkurin safarar jarirai 2

- Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya bankado wasu da suka yi yunkurin sace jarirai biyu

- jami'an kamfanin tare da jami'an tsaro sun zargi matafiyan ne bayan sun bada bayani mai karo da juna a kan jariran

- Da farko sun ce zasu isa Asaba kuma zasu tura yaran Ingila, daga bisani suka ce kasar Zimbabwe zasu aikasu

Jami'an kamfanin jirgin sama na Air Peace sun bankado wani yunkurin sace jarirai biyu a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mutum tare da wata mata ne suka kusa tafiya da yaran a ranar 7 ga watan Yunin 2021 a filin jirgin sama dake Legas.

An gano cewa matar da namjin na kan hanyarsu ne ta zuwa Asaba yayin da aka tsaresu domin duba kayansu.

KU KARANTA: Da duminsa: Babu sharadin da FG ta kafa na dage dakatar da Twitter

Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya bankado yunkurin safarar jarirai 2
Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya bankado yunkurin safarar jarirai 2. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon 'yar Najeriya dake siyar da shinkafa dafaffa ta N10, tace tana samun riba

Mai magana da yawun kamfanin jiragen saman, Stanley Olisa, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace jami'an kamfanin da na tsaro sun fahimci wani abu ba daidai ba yayin da ake duba fasinjojin.

Sun bada rahotanni masu sukar juna a kan jariran.

A wata takarda, ya ce: "A ranar 7 ga watan Yunin 2020 wurin karfe 12 na rana a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Legas, wata mace da namiji dauke da jarirai sun iso wurin duba fasinjoji.

"Jami'anmu sun zargi mutum biyun daga dabi'arsu kuma sun tambayesu kan jariran. Sun ce 'ya'yansu ne kuma zasu je Asaba ne tare."

Olisa ya bayyana cewa zargin yayi nisa bayan jami'an tsaro sun sake tambayarsu amma sai suka ce watan jariran uku kuma zasu Ingila ne.

Ya ce, "Mace da namijin sun bada magana mai karo da hakan bayan sun hadu da wasu jami'an. Sun ce zasu kai su Ingila ne wurin iyayensu, daga bisani suka ce Zimbabwe zasu aika dasu."

Bayan tuhumarsu da aka yi, sun tabbatar da cewa ba 'ya'yansu bane. Da gaggawa jami'an Air Peace suka kaisu ofishin 'yan sanda kuma za a mika su ga NAPTIP.

A wani labari na daban, sojoji masu mukamin Manjo Janar-janar kuma 'yan aji na 36 na makarantar horar da hafsin soji da aka bayyana za a yi musu ritayar dole bayan nada Manjo Najar Farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin kasa zasu gana da Yahaya tare da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Alhamis.

An tattaro cewa janarorin wadanda suke da ragowar shekaru uku na aiki sun koka da yadda basu zato balle tsammani ake nufo su da batun ritaya.

Sakamakon wannan cigaban, shugaban ma'aikatan tsaro ya gayyacesu wani taro domin su sasanta kan batun a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel