Kafin ku koma Ghana saboda Twitter, buhun shinkafarsu N48,000 ne, Hadimin Aisha Buhari

Kafin ku koma Ghana saboda Twitter, buhun shinkafarsu N48,000 ne, Hadimin Aisha Buhari

- Hadimi na musamman ga uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, yayi kira ga masu sukar gwamnati kan dakatar da Twitter

- Kamar yadda yace, ga masu son tattara komatsansu domin komawa kasar Ghana saboda Twitter, gara Najeriya sau dubu

- Ya bayyana yadda ake siyar da litar man fetur N393, kwalbar Coke N300 kuma ake siyar da buhun shinkafa a N48,000

Aliyu Abdullah, mataimaki na musamman ga uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, a fannin yada labarai da hulda da jama'a, yayi wata wallafa a kan dakatar da Twitter da gwamnatin tarayya tayi.

Idan zamu tuna, a makon da ya gabata ne ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed, ya sanar da hukuncin gwamnatin tarayya na dakatar da Twitter a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan goge wata wallafa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a shafinsa a kan 'yan ta'addan IPOB.

KU KARANTA: Dan sanda ya sheka lahira yayin da 'yan bindiga suka kashe manoma 41 a Zamfara

Kafin ku koma Ghana saboda Twitter, buhun shinkafarsu N48,000 ne, Hadimin Aisha Buhari
Kafin ku koma Ghana saboda Twitter, buhun shinkafarsu N48,000 ne, Hadimin Aisha Buhari. Hoto daga Lindaikejisblog.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Babu sharadin da FG ta kafa na dage dakatar da Twitter

A wallafar da yayi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 6 ga watan Yuni, ya rubuta:

"Gareku magauta, kafin ku tattara komatsanku domin komawa kasar Ghana saboda dakatar da Twitter, ina son sanar da ku cewa litar man fetur N393 ce, kwalbar Coke N300 take kuma buhun shinkafa N48,000 yake a Ghana."

Dakatar da Twitter a Najeriya ya janyo cece-kuce inda wasu suka takura kuma suke ganin gwamnatin tarayya ta takura su.

'Yan kasuwa sun koka inda suka ce hakan zai iya janyo musu fatara nan babu dadewa saboda nan suke tallata hajarsu.

Kafin ku koma Ghana saboda Twitter, buhun shinkafarsu N48,000 ne, Hadimin Aisha Buhari
Kafin ku koma Ghana saboda Twitter, buhun shinkafarsu N48,000 ne, Hadimin Aisha Buhari. Hoto daga Aliyu Abdullah
Asali: Facebook

A wani labari na daban, 'yan kasuwa a fadin kasar nan sun koka da yadda gwamnatin tarayya ta dakatar da Twitter a Najeriya inda suka ce kasuwancinsu a halin yanzu sun durkushe kuma akwai yuwuwa su fada rashin kudi.

Dakatarwan na nufin cewa 'yan kasuwan dake amfani da kafar wurin tallata hajarsu ga kwastomomi dole su daina tare da neman wata hanya ta daban.

Amma dukkan 'yan kasuwan da suka zanta da Nigerian Tribune sun ce babu wata kafar sada zumunta da ke basu irin wannan 'yancin kamar Twitter.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel