Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki

Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki

Shugaba Muhammadu Buhari na iya kasancewa mutum ba mai yawan magana ba, amma a bayyane yake cewa shugaban Najeriyan mutum ne mai son iyalinsa.

Wasu tsoffin hotunan shugaban kasar sun tabbatar da wannan da sauran abubuwa.

Wani abu da hotunan suka tabbatar shi ne cewa Shugaba Buhari mutum ne wanda ya sadaukar da kai sosai ga aikinsa.

Legit.ng ta gabatar da tsoffin hotuna guda bakwai na Shugaba Muhammadu Buhari

1. Masoyin Aisha Buhari

Soyayyarsa ga matarsa, Aisha Buhari, tana da ban sha'awa. Ana iya ganin shugaban kasar a cikin wani tsohon hoto tare da abar kaunarsa yayinda dukkansu suke sanye da kayan al'ada. Dan murmushin da Aisha tayi ya kayatar da hoton duk da cewa Buhari ya dake.

Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki
Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki Hoto: Opera News
Asali: UGC

2. Mutum ne mai son iyalinsa

Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai son iyalinsa wanda soyayyarsa ga matarsa da ‘ya‘yansa a bayyane take. A cikin hoton tuna bayan da ke a ƙasa, ana iya ganin Buhari da marigayiyar matarsa ​​Safinatu tare da yaransu.

Safinatu da yaranta biyu sun yi murmushi don daukar hoton yayinda shi kuma Buhari ya dake.

Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki
Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki Hoto: Opera News
Asali: UGC

3. Buhari mutum ne mai sadaukar da kai ga aiki

Muhammadu Buhari mutum ne da ya rike manyan mukamai. Ya kasance tsohon kwamishinan man fetur na tarayya, tsohon shugaban kasa a mulkin soja kuma shugaban kasa a yanzu.

A hoton da ke kasa, Buhari ya wakilci kasar a taron kungiyar Kasashe masu arzikin Man Fetur (OPEC).

Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki
Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki Hoto: Within Nigeria
Asali: UGC

4. Buhari dauke da daya daga cikin ‘ya’yansa mata

A karshe Muhammadu Buhari ya yi murmushi a hoto yayinda ya dauki 'yarsa a hannu. Wannan da wasu hotuna da yawa sun tabbatar da cewa shugaban Najeriya mutum ne mai son iyalinsa.

Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki
Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki Hoto: Within Nigeria
Asali: UGC

5. Buhari akan tafiyar aiki

An ga Muhammadu Buhari tare da Sheikh Ahmed Zaki Yamani na Saudiyya da Sarki Carl Gustaf na Sweden. An ɗauki hoton a taron OPEP na 13 ga watan Yuli, 1977.

Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki
Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki Hoto: AFP
Asali: Getty Images

6. Buhari ya je hutun bazara

Muhammadu Buhari ya je hutun bazara a makarantar Afirka ta Yamma a Ingila. Wasu dalibai sun rufa masa baya a cikin hoton.

Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki
Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki Hoto: Within Nigeria
Asali: UGC

7. Buhari tare da marigayiyar matarsa da yara

An ga Muhammadu Buhari tare da marigayiyar matarsa ​​Safinatu da ‘ya’yansu, Fatima, Hadiza da Zulaihat.

An ce an dauki hoton ne a Fadar Gwamnati, Barikin Dodan.

Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki
Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki Hoto: Flatimes
Asali: UGC

A baya mun ji cewa wani tsohon hoto na Shugaba Buhari yana more rayuwa lokacin da yake matashi ya haifar da zazzafan martani a shafukan sada zumunta.

Wani ma’abocin amfani da Facebook mai suna Ayo Ojeniyi ya dimauta yanar gizo da wani hoto wanda ba kasafai ake gani ba na Shugaba Buhari yayin da wani saurayi yake rawa da wata farar mace ba takalmi.

Buhari ya kasance dauke da murmushi yayin da suke rawa inda sauran matan da ke wurin suke kallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel