Yanzu-Yanzu: Hukumar Yan Sanda Ta Dakatar Da Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu

Yanzu-Yanzu: Hukumar Yan Sanda Ta Dakatar Da Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu

- Sufeta Janar na Yan sandan Nigeria, Usman Baba, ya sanar da dakatar da bada izinin amfani da gilashi mai duhu na motocci

- Usman Baba ya ce an gano wasu mutane na amfani da gilashin ne da lambar 'spy' wurin aikata abubuwan da ba su dace ba

- Shugaban yan sandan ya ce rundunar tana bita kan yadda za ta bullo da sabbin hanyoyin dakille matsalolin kafin a cigaba da bada izinin

Sufeta Janar na Rundunar Yan sandan Nigeria, Usman Baba, a ranar Litinin, ya bada umurnin dakatar da bada izinin amfani da gilashin mota mai duhu a fadin kasar baki daya, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma bada umarnin a dakatar da bada lambobin mota na masu leken asiri.

Yanzu-Yanzu: IGP Ya Haramta Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu
Yanzu-Yanzu: IGP Ya Haramta Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu
Asali: Original

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ɗan Kasuwa a Kano

Baba ya bada wannan umurnin ne a hedkwatar rundunar yan sanda da ke birnin tarayya, Abuja kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Majalisar harkokin yan sanda ta tabbatar da Baba a yayin da ya ke ganawa da kwamandojin yan sanda a kudu maso gabashin kasar kan hare-haren da ake kai wa yankin.

The Cable ta ruwaito cewa Babban sufetan na yan sanda ya ce an gano wasu na amfani da gilashin mai duhu da lambar sirrin wurin aikata abubuwan da ba su dace ba.

Ya yi bayanin cewa za a rika amfani da lambar sirrin na domin wasu wasu kamfanoni yayin da shi kuma gilashin mai duhu za a rika bada shi ne bisa wasu sabbin dokoki.

KU KARANTA: Dakarun Sojoji Sun Daƙile Hari, Sun Sheƙe Ƴan Bindiga a Hanyar Kaduna Zuwa Zaria

"Don haka, an dakatar da bada lambar sirri da gilashi mai duhu," in ji Baba.

"Ana bita kan dokokin bayar da su domin bullo da sabbin ka'idoji.

"A nan gaba za a fito da sabon tsari a bada lambar sirrin da kuma gilashi mai duhu da za a rika amfani da su a dukkan sassar kasar."

Babban sufetan na yan sanda ya jadada cewa an hana kafa shingen yan sanda kuma duk wani jami'i da aka kama yana aikata hakan zai fuskanci fushin hukuma.

Ya ce yadda jama'a ke rayuwa yana sauyawa don haka itama rundunar yan sandan za ta rika sauyawa da zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel