'Daliban KASU Sunyi Zanga-Zanga, Sun Tare Titin Zuwa Gidan Gwamna

'Daliban KASU Sunyi Zanga-Zanga, Sun Tare Titin Zuwa Gidan Gwamna

- Daliban jami'ar jihar Kaduna, KASU, sun yi zanga-zanga sun tare manyan tituna a jihar

- Daliban sun yi zanga-zangan ne domin karin kudin makaranta da mahukunta makarantar suka yi

- Daliban suna mika kokensu ne ga Gwamna Nasir El-Rufai ya saka baki a batun don a janye karin da suka ce mafi yawancinsu ba za su iya biya ba

Daliban Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, a ranar Talata sun tare babban titin zuwa gidan gwamnati a Kaduna, babban birnin jihar don yin zanga-zanga kan karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi, Channels Television ta ruwaito.

Jami'ar mallakar gwamnatin jihar ta sanar da karin kudin makaranta da kimanin 600% daga N26,000 da aka saba biya a baya.

Daliban KASU Sunyi Zanga-Zanga, Sun Tare Titin Zuwa Gidan Gwamna
Daliban KASU Sunyi Zanga-Zanga, Sun Tare Titin Zuwa Gidan Gwamna. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna

A cewar sabon tsarin kudin makarantar da aka gabatar, yan jihar za su rika biyan N150,000 yayin da abokan karatunsu a bangaren likitanci da kimiyya za su rika biyan N170,000 zuwa sama duk shekara.

A kan hakan ne daliban suka fito yin zanga-zanga suka rufe manyan titunan da za su bulla zuwa gidan gwamnati dauke da takardu masu sakonni daban-daban na nuna kin amincewarsu da karin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wannan zanga-zangar da daliban suka yi ya janyo cinkoson ababen hawa a wasu sassan jihar suna mai cewa dole gwamnatin jihar ta saurari kokensu ta biya musu bukatunsu.

Wasu daga cikin daliban sunyi addu'o'i a kan babban titin yayin da wasu daga cikinsu ke kula musu da titin.

Jami'an tsaro suma sun hallarci wurin zanga-zangar domin tabbatar da ana bin doka da oda.

Daliban sun koka da cewa karin da aka yi zai saka wasu da dama cikinsu su dena karatun domin ba za su iya biya ba.

KU KARANTA: Sabon Salo: 'Yan fashi sun fara zuwa sata gidajen mutane da na'urar POS

Don haka suke kira ga gwamnatin jihar ta janye karin kudin makarantar.

Sunyi kira ga Gwamna El-Rufai wanda ya ce cikin tsarinsa zai tabbatar yaran talakawa sunyi karatu ya saka baki cikin lamarin.

Jami'ar na da dalibai kimanin 19,000 cikinsu 17,000 yan asalin jihar ne.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel