An Kashe Sojoji 38, 'Yan Sanda 78 a Yankin Kudu Maso Gabas, Kwamandan Soja

An Kashe Sojoji 38, 'Yan Sanda 78 a Yankin Kudu Maso Gabas, Kwamandan Soja

- Birgediya Raymond Osoha, kwamandan sojojin Nigeria a jihar Imo, ya koka kan yadda ake kashe jami'an tsaro a kudu maso gabas

- Birgediya Osoha, ya ce rundunar sojojin kasa ta rasa dakarunta 38 yayin da rundunar yan sanda ta rasa jami'ai 78 a yankin

- Ya lissafa wasu hukumomin tsaron da suka rasa nasu jami'an yana mai cewa bai kamata a bar harkar tsaro hannun jami'an tsaron su kadai ba

Kwamandan Sojoji na 34 Brigade Artillery na Rundunar Sojojin Nigeria a Obinze, Birgediya Raymond Osoha, ya ce an kashe jami'an tsaro da dama a yankin kudu maso gabashin Nigeria sakamakon hare-haren da yan bindiga ke kaiwa.

Kwamandan sojojin ya yi wannan jawabin ne yayin wani taro da kwamishinan rundunar yan sandan jihar Imo ya kira a ranar Asabar kamar yadda Tribune ta ruwaito.

An Kashe Sojoji 38, Yan Sanda 78 a Yankin Kudu Maso Gabas, Kwamandan Soja
An Kashe Sojoji 38, Yan Sanda 78 a Yankin Kudu Maso Gabas, Kwamandan Soja. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: El-Rufai Ya Ɗauki Sabbin Ma'aikata '10,000' a Yayin Da Jihar Ke Rage Ma'aikata

Osoha ya ce sojojin kasa 38 ne suka rasu yayin da yan sanda 78 ne suka rasa rayyukansu a yankin na kudu maso gabas.

A cewarsa, sojojin ruwa biyar sun mutu, sojojin sama bakwai yayin da jami'an NSCDC 15 da jami'an yan sandan unguwa 31 suka rasu.

Ya ce kallubalen tsaron da kasar ke fuskanta a halin yanzu ba abin da za a bar jami'an tsaro bane kawai su kadai.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar Yan Sanda Ta Dakatar Da Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu

Kwamandan na sojojin ya ce dakarun sojoji su kan kwashe awanni a cikin rana da ruwan sama a yayin da suke aikin tsare lafiya da dukiyoyin jama'a.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164