Stephen Akinola: Wani shahararren faston Najeriya ya mutu awanni Bayan mutuwar TB Joshua

Stephen Akinola: Wani shahararren faston Najeriya ya mutu awanni Bayan mutuwar TB Joshua

- Mabiya darikar Redemption Ministries Worldwide suna jimamin mutuwar babban limaminsu, Reverend Stephen Akinola

- Mutuwar Reverend Akinola na zuwa ne yayinda mabiya addinin kirista a Najeriya ke fama da radadin mutuwar Prophet TB Joshua

- Cocin Redemption Ministries Worldwide na da hedikwatarta a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas

Reverend Stephen Akinola, babban jagoran cocin Redemption Ministries Worldwide ya mutu.

BBC ta ruwaito cewa shahararren faston da ke zaune a jihar Ribas ya mutu a safiyar Lahadi, 6 ga watan Yuni. Jaridar ta bayyana cewa daya daga cikin fastocinsa ne ya tabbatar da mutuwar Akinola.

KU KARANTA KUMA: 2023: Atiku ya mayar da martani game da kudirinsa na shugabancin kasa, ya magantu kan fastocinsa da Soludo

Stephen Akinola: Wani shahararren faston Najeriya ya mutu awanni Bayan mutuwar TB Joshua
Stephen Akinola: Wani shahararren faston Najeriya ya mutu awanni Bayan mutuwar TB Joshua Hoto: Stephen Akinola
Asali: Facebook

Majiyar ta ce:

"Cocin ta sanar da dukkanin fastocin afkuwar lamarin kuma an ijiye gawar sa a dakin ijiye gawar."

Labarin mutuwar Akinola ya zo ne sa’o’i kadan bayan mutuwar Prophet TB Joshua, wanda ya kafa Cocin Synagogue Church of All Nations.

KU KARANTA KUMA: Duk wani Gwamna da ya bar PDP, ya shiga APC zai sha mamaki – Gwamnan Benuwai

Al’ummar kirista suna jimamin mutuwar Akinola

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa mambobin kungiyar Redemption Ministries sun yi dafifi zuwa cocin wanda ke da hedikwata a Fatakwal domin jimamin mutuwar shahararren malamin.

Apostle Eugene Ogu, tsohon shugaban kungiyar Pentikostal Fellowship of Nigeria (PFN) ya bayyana mutuwar Akinola a matsayin abin bakin ciki.

Ya ce:

“Ee, wannan rana ce ta bakin ciki ga al’ummar kirista. Yayin da muke kan magana game da Prophet TB Joshua, mutuwar Akinola ta faru.
“Abin bakin ciki ne. Ina rokon Allah ya ba Kristi gaba daya dangana domin shi (Akinola) ya yi aiki sosai domin Yesu.''

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalai da mabiya fastor Temitope Balogun wanda aka fi sani da TB Joshua kan mutuwarsa.

Shugaban ya ce za a yi kewar fitataccen malamin na Kirista musamman mabiyansa da kuma duniya baki daya kan gudunmuwarsa ga mutane ta hanyar ayyukansa na taimako.

Ya kuma jajantawa gwamnati da mutanen jihar Ondo kan rashin da suka yi na Fasto TB Joshua.

Asali: Legit.ng

Online view pixel