El-Rufa'i da wani gwamnan APC sun bijirewa umarnin Buhari na hana Twitter

El-Rufa'i da wani gwamnan APC sun bijirewa umarnin Buhari na hana Twitter

- Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnonin APC biyu sun bijirewa umarnin gwamnati na dakatar da Twitter

- An ga rubutun gwamnonin biyu biyo bayan dakatar da ayyukan Twitter a fadin kasar ta Najeriya

- Sai dai, an bayyana wasu dalilai da suka ja wadannan gwamnoni suka yi amfani da shafin na Twitter

Biyo bayan umarnin gwamnatin tarayya na dakatar ayyukan Twitter a Najeriya, an samu wasu gwamnonin Najeriya da suka yi kunnen kashi suka yi rubutu a shafin na Twitter.

Gwamnonin jihohin Kaduna da Ondo, Nasir El-Rufai da Rotimi Akeredolu, suka bijirewa wannan umarni na gwamnati, Premium Times ta ruwaito.

Dukkanin gwamnonin, wadanda suke mambobin jam’iyyar APC mai mulki, sun yi rubutun a Twitter, ba tare da tsoron barazanar Babban Lauyan Tarayya da Ministan Shari’a, Abubakar Malami na hukunta masu yin Twitter ba.

El-Rufai, daidai karfe 9:37 na dare a ranar Lahadi, ya ba da labarin ra'ayi mai taken “Based Nigeria: African country teaches US lesson in how to handle Big Tech tyranny”.

KU KARANTA: Dillalan albasa za su katse kai kaya zuwa Kudancin Najeriya daga ranar Litinin

El-Rufa'i da wani gwamnan APC sun bijirewa umarnin Buhari na hana Twitter
El-Rufa'i da wani gwamnan APC sun bijirewa umarnin Buhari na hana Twitter Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Labarin wanda Nebojsa Malic, wani dan jarida Ba-Amurke ne ya wallafa, ya ba da dalilin dakatar da shafin na Twitter, inda ya ja hankalin Amurka don daukar darasi daga matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka.

Gwamna Akeredolu, a daya bangaren kuwa, ya fitar da sanarwa dangane da wani harin wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama a yankin Igangan da ke jihar Oyo a ranar Lahadi.

Ya yi magana ne kan kashe-kashen a matsayinsa na Shugaban kungiyar Gwamnonin Kudu maso Yamma.

“Mu, a namu bangaren, mun yanke shawarar kare mutanenmu, da dukiyoyinsu, da duk wata hanyar da ta dace ciki da na waje. A kan wannan, ba za a yi sulhu ba," sanarwar ta karanta.

Majiyoyin gwamnati sun shaida cewa Gwamna El-Rufai ya kasance a wajen kasar sama da mako guda. Duk da cewa majiyar ba ta bayyana inda yake ba, amma ta ce "ba a dakatar da ayyukan Twitter a kasar ba."

Lokacin da aka tuntube shi, kakakin Gwamna Akeredolu, Olabode Richard, ya ce 'yan Najeriya na iya hawa kafar Twitter a ranar Lahadi, ya kara da cewa shugaban na sa bai yi amfani da Virtual Private Network (VPN) ko wasu hanyoyin da 'yan Najeriya ke bi ba.

KU KARANTA: Tuna baya: Hotunan marigayi TB Joshua na aikin alheri sun bar mutane cikin jimami

A wani labarin daban, An shiga fargaba a garin Igangan, jihar Oyo, a daren Asabar, 5 ga Yuni, yayin da wasu 'yan bindiga suka tura sama da mutane 45 zuwa kabari.

Sun News ta ruwaito cewa barnar da aka kwashe sa’o’i biyar ana yi a daya daga cikin manyan garuruwan Ibarapaland ta kai ga kone gidaje sama da 60, yayin da sama da motoci 160 kuma suka lalace.

Maharan sun yi kaca-kaca da fadar Ashigangan ta Igangan, Oba Lasisi Adeoye, da kuma wani gidan mai, yayin da suka afka wa al'ummar da misalin karfe 11 na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel