Shugaba Buhari ya shiga matukar jimamin mutuwar TB Joshua

Shugaba Buhari ya shiga matukar jimamin mutuwar TB Joshua

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa ga mutuwar malamin addinin Kirista, TB Joshua

- Ya bayyana cewa, lallai mabiyansa da ma kasa baki daya za ta yi kewar fitaccen malamin na Kirista

- Hakazaila ya ba dangi da mabiyansa hakuri bisa rashin, yana mai lallashi da tausasa zukatansu

Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalai da mabiya fastor Temitope Balogun wanda aka fi sani da TB Joshua kan mutuwarsa.

Shugaban ya ce za a yi kewar fitataccen malamin na Kirista musamman mabiyansa da kuma duniya baki daya kan gudunmuwarsa ga mutane ta hanyar ayyukansa na taimako.

Ya kuma jajantawa gwamnati da mutanen jihar Ondo kan rashin da suka yi na Fasto TB Joshua.

KU KARANTA: Bayan shekaru 5 na aiki tukuru, beran da ya ci lambar yabon zinare ya yi ritaya

Shugaba Buhari ya shiga matukar jimamin mutuwar TB Joshua
Shugaba Buhari ya shiga matukar jimamin mutuwar TB Joshua Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Fitaccen mai wa'azin na Kiristoci a Najeriya TB Joshua ya mutu ne ranar Asabar da daddare a birnin Lagos yana da shekaru 57 a duniya.

A wata sanarwa da Legit.ng Hausa daga gano da aka fitar daga fadar shugaban kasa tana bayyana jimamin shugaban da cewa:

"Shugaba Buhari ya bukaci mabiyan Fasto Joshua da su yi hakuri tare da sanin cewa ba a auna rayuwa da ma'ana ta tsawon rayuwa sai dai ta hanyar jure wa da kuma sauya rayuwar al'umma da aka yi."

KU KARANTA: An dakile harin 'yan ta'adda a hedkwatar 'yan sanda ta Imo, an hallaka tsageru 5

A wani labarin, Wanda ya ƙirƙiro majami'ar dukkan ƙasashe, Fasto Temitope Balogun Joshua, da aka fi sani da T. B Joshua ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 57, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

An fara raɗe-raɗin mutuwar fitaccen malamin majami'ar da sanyin safiyar Lahadi, amma daga baya majami'ar ta tabbatar, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa 7 game da marigayi T. B Joshua.

Asali: Legit.ng

Online view pixel