Matan Gwamnoni Sun Yi Magana Kan Matsalar Tsaro, Rashin Aikin Yi, Da Talaucin da Yan Najeriya Suke Ciki

Matan Gwamnoni Sun Yi Magana Kan Matsalar Tsaro, Rashin Aikin Yi, Da Talaucin da Yan Najeriya Suke Ciki

- Ƙungiyar matan gwamnonin ƙasar nan, sun nuna matuƙar damuwarsu da halin rashin tsaron da talakawa ke ciki

- Shugabar ƙungiyar, Bisi Fayemi, itace ta bayyana haka a Abuja, jim kaɗan bayan fitowa daga taron da suka gudanar

- Tace ita da sauran yan uwanta zasu haɗa ƙarfi da karfe tare da taimakon mazajen su wajen inganta rayuwar talaka

Matan gwamnonin ƙasar nan ƙaraƙashin ƙungiyarsu sun bayyana matuƙar damuwarsu kan karuwar matsalar tsaro a faɗin Najeriya tare da talaucin da ya addabi yan ƙasa, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Gana da Sabon Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya

Saboda haka, matan sun bayyana cewa zasu haɗa hannu da mazajen su, Gwamnoni, domin magance duk wani ƙalubalen da ya taso.

Shugabar ƙungiyar, Bisi Fayemi, matar gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ita ce ta bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan fitowar su daga taro a sakateriyar NGF dake Abuja.

Matan Gwamnoni Sun Yi Magana Kan Matsalar Tsaro, Rashin Aikin Yi, Da Talaucin da Yan Najeriya Suke Ciki
Matan Gwamnoni Sun Yi Magana Kan Matsalar Tsaro, Rashin Aikin Yi, Da Talaucin da Yan Najeriya Suke Ciki Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tace: "Muna matuƙar damuwa da halin tsaron da ƙasar mu ke ciki, da kuma mummunar shafan mata da ƙananan yara da yanayin yayi."

"Hakanan kuma mun damu da yawaitar rashin aikin yi, wanda yasa matasa ke zaman kashe wando, babu aikin yi."

"Sannan mun damu da talaucin da ya addabi mata musamman waɗanda ke rayuwa a ƙauyukan ƙasar nan."

KARANTA ANAN: Babbar Magana: FG Ta Gayyaci Jakadun Amurka, Burtaniya Kan Maganar da Sukayi Bayan Hana Amfani da Twitter

Mrs. Fayemi ta ƙara da cewa yan uwanta matan gwamnoni a shirye suke su taimakawa gwamnatocin jihohin su domin ganin an samar da rayuwa mai inganci ga yan ƙasa.

Tace ita da sauran takwarorin ta zasu yi dukkan mai yuwu wa tare da haɗin guiwar mazajen su domin tabbatar da an inganta rayuwar talaka.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

Shugaban Ƙasa Buhari ya ƙaddamar da sabuwar makarantar Chibok da aka sake ginawa kuma aka canza mata suna, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban wanda ministan mata, Mrs Pauline Tallen, ta wakilta, yace gwamnatinsa na iya ƙoƙarinta wajen ganin komai ya daidaita a garin Chibok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel