Dakatar da Twitter a Najeriya zai iya jefamu fatarar kudi, 'Yan kasuwa
- 'Yan kasuwa na kasar Najeriya na cigaba da kokawa kan dakatar da twitter da gwamnatin tarayya tayi
- Sun bayyana cewa a Twitter ne suke tallata hajojinsu kuma a nan suke samun masu siya har suke rayuwa
- Wani dalibi dan kasuwa ya bayyana yadda karatunsa zai iya tsayawa saboda a Twitter yake talla har ya samu na makaranta
'Yan kasuwa a fadin kasar nan sun koka da yadda gwamnatin tarayya ta dakatar da Twitter a Najeriya inda suka ce kasuwancinsu a halin yanzu sun durkushe kuma akwai yuwuwa su fada rashin kudi.
Dakatarwan na nufin cewa 'yan kasuwan dake amfani da kafar wurin tallata hajarsu ga kwastomomi dole su daina tare da neman wata hanya ta daban.
Amma dukkan 'yan kasuwan da suka zanta da Nigerian Tribune sun ce babu wata kafar sada zumunta da ke basu irin wannan 'yancin kamar Twitter.
KU KARANTA: Da duminsa: T. B Joshua ya rasu, yana da shekaru 57 a duniya
KU KARANTA: King of Dragons: Jami'an tsaro a Imo sun sheke hatsabibin shugaban IPOB/ESN
Karatuna yana cikin wani hali
Elijah Peter dalibi ne dake digiri na biyu a daya daga cikin jami'o'in Najeriya. Ya sanar da cewa yana siyar da takalma kuma da Twitter ya dogara wurin tallata hajarsa.
Daga abinda yake samu, shine yake daukar dawainiyar karatunsa. "Twitter ta zama babban jigo wurin hada ni da kwastomomina na shekaru uku. Ta hada ni da kwastomomi fiye da WhatsApp da Facebook. A gaskiya wannan dakatarwan ta shafi karamin kasuwanci na."
Wadanda suka zuba hannayen jari a kasuwancina zasu zo karbar riba
Aisha Shittu na siyar da takalma da jakkuna a Twitter. Ta ce: "Twitter tana da fadi kuma ta taimaka min wurin habaka kasuwanci na ba kadan ba. Twitter ta bada gudumawar kashi 40 na cigaban kasuwancina."
Amma kuma tace wannan cigaban zai durkushe nan babu dadewa saboda wadanda suka zuba hannayen jari a kasuwancin kuma tana basu riba kowanne wata sun kusa zuwa karbar kason su.
A wani labari na daban, manyan sojoji ashirin da tara aka tirsasa yin murabus daga aiki bayan nada Manjo Janar farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya.
Wannan tirsasa murabus din ya ci karo da ikirarin hedkwatar tsaro na makon da ya gabata wanda suka ce babu sojan da za a yi wa ritaya duk da nada Yahaya a matsayin shugaban sojin kasa da Buhari yayi.
Yahaya mai mukamin Manjo Janar daga jihar Sokoto ya samu mukamin shugaban sojin kasa na Najeriya a ranar 27 ga watan Mayu bayan mutuwar Ibrahim Attahiru.
Asali: Legit.ng