King of Dragons: Jami'an tsaro a Imo sun sheke hatsabibin shugaban IPOB/ESN

King of Dragons: Jami'an tsaro a Imo sun sheke hatsabibin shugaban IPOB/ESN

- Jami'an tsaro sun cigaba da bibiyar mambobin IPOB da ESN dake kaiwa 'yan sanda farmaki a yankin kudu maso gabas

- Mai magana da yawun rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ya bayyana yadda sojoji suka sheke mambobin kungiyar

- Rundunar sojin kasan Najeriya tayi kira ga 'yan kasa da su tallafawa jami'an tsaro wurin yakar kalubalen tsaro a kasar nan

Owerri, jihar Imo

Dakarun sojin kasa na Najeriya sun harbe wani babban kwamandan ESN, kungiyar miyagun 'yan ta'adda dake rajin karbar kasar Biafra a babban birnin jihar Imo, Owerri.

Birgediya Janar Mohammed Yerima, mai magana da yawun rundunar a wata takarda ta ranar Lahadi, 6 ga watan Yuni ta shafinsu na Facebook, ya bayyana sunan kwamandan da aka kashe da Joseph Uka Nnachi, wanda aka fi sani da King Of Dragons.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai farmaki Kano, sun yi luguden wuta tare da sace attajiri

King of Dragons: Jami'an tsaro a Imo sun sheke hatsabibin shugaban IPOB/ESN
King of Dragons: Jami'an tsaro a Imo sun sheke hatsabibin shugaban IPOB/ESN. Hoto daga Audu Marte/ Issouf Sanogo
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Da duminsa: Bayan Twitter, Facebook ta goge tsokacin Buhari kan yakin basasa da ya janyo cece-kuce

Yerima ya sanar da cewa dakarun sojin da suka samu tallafin jami'an runduna ta musamman ta 'yan sanda sun halaka Dragon tare da wasu mambobi hudu bayan jami'an tsaro sun fatattaki wadanda suka kaiwa ofishin 'yan sanda hari.

Yace marigayin kwamandan ya dinga shugabantan hare-hare kan jami'an tsaro da sansaninsu a yankin kudu maso gabas.

Kamar yadda rundunar sojin kasa tace, an samu wasu kayayyaki daga wadanda ake zargi da suka hada da bindigogi kirar AK47 hudu, mota kirar Toyota Hiace karamar bas tare da miyagun makamai da layu.

Rundunar sojin Najeriya ta yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da baiwa jami'an tsaro tallafi da goyon baya domin samun shawo kan matsalar tsaro a yankin kudu maso gabas da fadin Najeriya baki daya.

A wani labari na daban, Twitter ta bayyana tsananin damuwarta bayan hukuncin gwamnatin tarayya na dakatar da ayyukanta a Najeriya.

Sarah Hart, babbar manajan yada labarai ta Twitter na Turai, gabas ta tsakiya da Afrika ta sanar da TheCable cewa kamfanin na duba wannan cigaban.

TheCable ta ruwaito yadda gwamnati ta dakatar da ayyukanta bayan zargin kafar sada zumuntar da goge wani tsokacin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: