Sunaye: Bayan nadin sabon COAS, rundunar soji ta yi wa manyan sojoji 29 ritayar dole

Sunaye: Bayan nadin sabon COAS, rundunar soji ta yi wa manyan sojoji 29 ritayar dole

- Rundunar soji ta yi wa manyan hafsan sojoji 29 ritaya duk da musantawa da hedkwatar tsaro tayi

- A wata takarda, rundunar ta amince da izinin hutun manyan sojojin 29 wanda daga nan zasu yi ritaya bayan nadin Yahaya

- Daga cikin wadanda aka yi wa ritayar karfi da yajin akwai AA Sarham, BM Shafa, UM Mohammed da wasu manyan sojoji 26

Manyan sojoji ashirin da tara aka tirsasa yin murabus daga aiki bayan nada Manjo Janar farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya.

Wannan tirsasa murabus din ya ci karo da ikirarin hedkwatar tsaro na makon da ya gabata wanda suka ce babu sojan da za a yi wa ritaya duk da nada Yahaya a matsayin shugaban sojin kasa da Buhari yayi.

Yahaya mai mukamin Manjo Janar daga jihar Sokoto ya samu mukamin shugaban sojin kasa na Najeriya a ranar 27 ga watan Mayu bayan mutuwar Ibrahim Attahiru.

KU KARANTA: Da duminsa: Bayan Twitter, Facebook ta goge tsokacin Buhari kan yakin basasa da ya janyo cece-kuce

Sunaye: Bayan nadin sabon COAS, rundunar soji ta yi manyan sojoji 29 ritaya
Sunaye: Bayan nadin sabon COAS, rundunar soji ta yi manyan sojoji 29 ritaya. Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Twitter ta yi martani bayan dakatar da ayyukanta a Najeriya, ta sanar da matakin dauka

A wata takarda da Premium Times ta gani, ta nuna cewa an amincewa sojoji masu mukamin manjo janar 29 su tafi hutu, lamarin da zai bude hanyar ritayarsu.

Wannan ritayar ta zo ne kasa da makonni biyu bayan nada Yahaya a matsayin shugaban rundunar.

Ga jerin sunayensu:

1. JB Olawumi

2. JO Akomolafe

3. CO Ude

4. G Oyefesobi

5. MO Uzoh

6. CC Okonkwo

7. MSA Aliyu

8. UM Mohammed

9. BM Shafa

10. NE Angbazo

11. YP Auta

12. SA Yaro

13. J Sarham

14. HE Ayamasoawei

15. OF Azinta

16. BA Akinroluyo

17. KAY Isiyaku

18. AT Hamman

19. AM Aliyu

20. HPZ Vintienagba

21. HR Momoh

22. JR Unuigbe

23. AA Jidda

24. OI Uzomere

25. MH Magaji

26. LA Adegboye

27. MA Masanawa

28. OA Akinyemi

29. AM Dauda

A wani labari na daban, kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana dalilinta na kashe shugaban kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, Abubakar Shekau, Daily Nigerian ta ruwaito.

A wani sakon cikin gida daga shugaban ISWAP, Abu Musab Albarnawi, wanda jaridar HumAngle ta samu a ranar Juma'a, ya ce Shekau ya kashe kansa ne bayan kin mika kai da yayi sakamakon kutsen da aka yi a maboyarsu a ranar 19 ga watan Mayun 2021.

Shugaban ISWAP yace shugaban rikon kwarya na ISIS na Iraq da Syria ya bada umarnin su dauka mataki kan Shekau saboda bijire musu da kuma kashe "masu imani" da yake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng