Dan sanda ya sheka lahira yayin da 'yan bindiga suka kashe manoma 41 a Zamfara
- 'Yan bindiga a jihar Zamfara sun halaka manoma 41 tare da sheke dan sanda daya
- Miyagun sun kai hari kauyukan Tofa da Samawa inda suka far wa manoma a gonakinsu
- An gano cewa 'yan bindigan basu saci komai ba a kauyukan, illa iyaka kisan da suka yi
'Yan bindiga sun sake kashe manoma 41 a kauyukan Tofa da Samawa na karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin wanda yace sunansa Malam Balarabe, ya sanar da The PUNCH cewa 'yan bindigan sun kutsa yankin yayin da manoman ke gonakinsu suna shuka, wasu kuma suna gyaran gona.
"Kwatsam suka bayyana sannan suka dinga harbin manoman inda suka kashe da yawa daga ciki," Balarabe ya jaddada.
Ya kara da yin bayanin cewa 'yan bindigan sun kara da rufe titunan da zasu sada jama'a zuwa kauyukan biyu inda suka kashe wasu manoman dake komawa gida.
KU KARANTA: Da duminsa: Twitter ta yi martani bayan dakatar da ayyukanta a Najeriya, ta sanar da matakin dauka
KU KARANTA: Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana dalilin da yasa ta kashe Shekau har lahira
Balarabe yace manoma 41 ne suka rasa rayukansu inda ya kara da cewa 'yan bindigan basu dauka komai daga kauyukan biyu ba.
"Sun je yin kisa ne kawai kuma manoman dake gona suka je kashewa," Balarabe ya kara da cewa.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya ce, "Rundunar hadin guiwa ta 'yan sandan bata san da labarin ba sai bayan 'yan bindigan sun gama kashe-kashe a yankin Tofa. Har yanzu bamu san yawan wadanda suka kashe ba."
"Amma kuma, yayin da 'yan bindigar suka bar Tofa suna kan hanyar kauyen Samawa domin kai wani hari, 'yan sandan dake kauyen Samawa sun gaggauta isa tare da musayar luguden wuta da 'yan bindigan.
“A sakamakon arangamar, an kashe 'yan bindigan da ba a san yawansu ba yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika. Ba a samu rashin rai ko daya ba a garin Samawa. Sai dai dan sanda daya ya amsa kiran Ubangijinsa," Shehu yace.
A wani labari na daban, kamfanin Twitter ya nuna shirinsa na taimakon 'yan Najeriya wurin amfani da kafar sada zumuntar duk da gwamnatin tarayya ta dakatar da hakan.
A wata takarda da ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya fitar a ranar Juma'a, ya sanar da dakatarwan inda yace ana amfani da kafar wurin kaskanci tare da muzgunawa Najeriya.
Amma martani da aka yi wa kasar bayan dakatarwan, Twitter ta wallafa cewa zata yi duk abinda ya dace wurin baiwa 'yan Najeriya damar amfani da kafar.
Asali: Legit.ng