Twitter ta sha alwashin ba 'yan Najeriya damar amfani da ita duk da Buhari ya dakatar

Twitter ta sha alwashin ba 'yan Najeriya damar amfani da ita duk da Buhari ya dakatar

- Kamfanin Twitter ya sha alwashin baiwa 'yan Najeriya damar amfani da kafar duk da gwamnati ta dakatar

- Kamar yadda manhajar mai tambarin tsuntsu ta bayyana, ta matukar damuwa da dakatarwar da aka yi mata a Najeriya

- A ranar Juma'a ne ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed, ya sanar da dakatar da kafar a Najeriya

Kamfanin Twitter ya nuna shirinsa na taimakon 'yan Najeriya wurin amfani da kafar sada zumuntar duk da gwamnatin tarayya ta dakatar da hakan.

A wata takarda da ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya fitar a ranar Juma'a, ya sanar da dakatarwan inda yace ana amfani da kafar wurin kaskanci tare da muzgunawa Najeriya.

Amma martani da aka yi wa kasar bayan dakatarwan, Twitter ta wallafa cewa zata yi duk abinda ya dace wurin baiwa 'yan Najeriya damar amfani da kafar.

KU KARANTA: 'Yan bindiga 5 sun hadu da ajalinsu bayan sun yi arangama da 'yan sanda a Katsina

Twitter ta sha alwashin ba 'yan Najeriya damar amfani da ita duk da Buhari ya dakatar
Twitter ta sha alwashin ba 'yan Najeriya damar amfani da ita duk da Buhari ya dakatar. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gagararriyar kungiyar fashi da makami ta mutum 3 ta shiga hannun 'yan sanda a Ribas

"Mun matukar damuwa da toshe Twitter da aka yi a Najeriya. Samun kafar yanar gizo kyauta kuma budaddiya babban hakki ne na dan Adam a zamanin nan.

"Zamu yi kokarin ganin cewa mun dawowa 'yan Najeriyan da su dogara da Twitter domin sadarwa," Kamfani ya wallafa a ranar Asabar.

A wani labari na daban, hedkwatar tsaron Najeriya ta ce rade-radin da ake na cewa akwai yuwuwar ritayar wasu sojoji masu mukamin janar-janar bayan nadin da shugaban kasa yayi wa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban sojin kasa, ba gaskiya bane.

Mukaddashin daraktan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Abuja a ranar Alhamis, Daily Nigerian ta ruwaito.

Onyeuku yace murabus din wasu manyan hafsoshin sojoji a rundunar na sa kai ne, kari da cewa har yanzu rundunar bata aminta da ritayar wani hafsan soja ba.

"A wannan lokacin, dukkanku kun san nadin da aka yi wa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojin kasa.

"Wannan ya janyo rade-radi daga kafafen yada labarai akan yadda za a kakkabe wasu manya a rundunar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel