Da duminsa: Twitter ta yi martani bayan dakatar da ayyukanta a Najeriya, ta sanar da matakin dauka

Da duminsa: Twitter ta yi martani bayan dakatar da ayyukanta a Najeriya, ta sanar da matakin dauka

- Twitter ta bayyana damuwarta a kan hukuncin gwamnatin tarayya na dakatar da ayyukanta a kasar Najeriya

- Kamar yadda jami'ar yada labarai na Turai, gabas ta tsakiya da Afrika ta sanar, kamfanin yana bincike kuma zai sanar da matakin gaba

- A ranar Juma'a ne ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya sanar da hukuncin gwamnatin tarayya na dakatar da ayyukan Twitter

Twitter ta bayyana tsananin damuwarta bayan hukuncin gwamnatin tarayya na dakatar da ayyukanta a Najeriya.

Sarah Hart, babbar manajan yada labarai ta Twitter na Turai, gabas ta tsakiya da Afrika ta sanar da TheCable cewa kamfanin na duba wannan cigaban.

TheCable ta ruwaito yadda gwamnati ta dakatar da ayyukanta bayan zargin kafar sada zumuntar da goge wani tsokacin shugaban kasa.

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta magantu kan hasashen ritayar dole ga manyan sojoji

Da duminsa: Twitter ta yi martani bayan dakatar da ayyukanta a Najeriya, ta sanar da matakin dauka
Da duminsa: Twitter ta yi martani bayan dakatar da ayyukanta a Najeriya, ta sanar da matakin dauka. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon mutumin da ya dako tsalle daga jirgin sama babu kumbo, ya kafa tarihi a duniya

A wata takarda da Lai Mohammed, ministan yada labarai ya fitar a ranar Juma'a, yace dole ce ta sa gwamnati ta yi abinda tayi saboda ana amfani da kafar wurin kaskanci ga Najeriya.

Amma kuma har a lokacin rubuta wannan rahoton, kafar na nan tana aiki a Najeriya.

A wani sakon yanar gizo, Hart ta ce: "Sanarwan da Najeriya tayi na dakatar da ayyukanta a Najeriya abun damuwa ne.

"Muna bincike kuma zamu sanar da halin da ake ciki idan muka kammala."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kushe yadda wasu bata-gari ke kaiwa kadarorin gwamnati hari a yankunan kasar nan. Ya yi barazanar yi musu amfani da abinda suka fi ganewa inda ya alakanta hakan da yakin basasa.

A wani labari na daban, an tabbatar da kisan 'yan bindiga biyar a yammacin Laraba yayin da suka yi arangama da rundunar 'yan sanda a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan da zasu kai dari da hamsin sun tsinkayi kauyukan Wurma da Yarbudu, jaridar ThisDayLive ta ruwaito.

Amma kuma 'yan sandan dake kauyen Wurma sun yi gaba da gaba da 'yan bindigan. Majiya daga rundunar 'yan sandan tace daya daga cikin 'yan bindigan ya sheka lahira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel