Babbar Magana: FG Ta Gayyaci Jakadun Amurka, Burtaniya Kan Maganar da Sukayi Bayan Hana Amfani da Twitter

Babbar Magana: FG Ta Gayyaci Jakadun Amurka, Burtaniya Kan Maganar da Sukayi Bayan Hana Amfani da Twitter

- Gwamnatin tarayya da gayyaci jakadun Amurka, Burtaniya da sauransu kan maganar da suka yi bayan an hana hawa twitter

- Ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, shine ya gayyace su domin su tattauna game da batun

- Matakin gwamnatin tarayya na hana hawa twitter na cigaba da ɗaukar hankalin yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta gayyaci jakadun ƙasashen Amurka, Burtaniya, Canada da ƙungiyar tarayyar turai bisa maganar da suka yi akan matakin gwamnati na hana amfani da twitter, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

Ƙasashen sun nuna rashin amincewarsu kan matakin gwamnatin, inda suka bayyana shi da tauye haƙƙin yan Najeriya na faɗin ra'ayoyin su.

Babbar Magana: FG Ta Gayyaci Jakadun Amurka, Burataniya Kan Maganar da Sukayi Bayan Hana Amfani da Twitter
Babbar Magana: FG Ta Gayyaci Jakadun Amurka, Burataniya Kan Maganar da Sukayi Bayan Hana Amfani da Twitter Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani jawabi da ma'aikatar harkokin kasashen waje ta fitar ta hannun, Kimiebi Ebienfa , dake sashin hulɗa da jama'a na ma'aikatar, ya kira yi jakadun su zo domin tattaunawa da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: NBC Ta Umarci Dukkan Tashoshin Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter

Wani ɓangaren Jawabin yace:

"An umarce ni da in sanar daku cewa biyo bayan jawaban da wasu jakadun ƙasashen waje a Najeriya suka yi kan hana amfani da twitter da FG tayi, ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, yana gayyatar waɗanda abun ya shafa zuwa taron da zai gudana yau da misalin ƙarfe 12:00 na rana."

"Wurin da za'a gudanar da taron shine ɗakin taron minista dake ma'aikatar harkokin waje, a hawa na takwas."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

Shugaban Ƙasa Buhari ya ƙaddamar da sabuwar makarantar Chibok da aka sake ginawa kuma aka canza mata suna, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban wanda ministan mata, Mrs Pauline Tallen, ta wakilta, yace gwamnatinsa na iya ƙoƙarinta wajen ganin komai ya daidaita a garin Chibok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262