An Kuma, Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Aƙalla 27 a Jihar Benuwai

An Kuma, Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Aƙalla 27 a Jihar Benuwai

- Wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari wani ƙauye a jihar Benuwai, inda suka kashe mutum 27

- Mazauna ƙauyen sun shaida wa yan jarida ta wayar salula cewa maharan sun shigo garin ne da yammacin ranar Lahadi

- Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Adoyi Sule, yace ya ziyarci ƙauyen kuma a binciken da ya gudanar maharan sun kashe aƙalla mutum 27

Wasu yan bindiga sun hallaka aƙalla mutum 27 a ƙauyen Odugbeho, ƙaramar hukumar Agatu, jihar Benuwai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

Yan bindigan sun kai hari ƙauyen ne ranar Lahadi da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

A halin yanzun an gano gawarwakin mazauna ƙauyen aƙalla 27 bayan harin da aka kai musu.

An Kuma, Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Aƙalla 27 a Jihar Benuwai
An Kuma, Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Aƙalla 27 a Jihar Benuwai Hoto: Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wasu mazaunan ƙauyen sun shaidawa dailytrust ta wayar salula cewa, yan bindigan sun shiga ƙauyen da yamma inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Wani shaidan gani da ido mai suna, Onehi, ya bayyana cewa an gano gawarwaki 11 da daren ranar da aka kawo harin, yayin da aka gano sauran da safiyar Litinin.

Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Adoyi Sule, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace adadin waɗanda aka kashe a halin yanzun yakai 27, kuma ana cigaba da bincike.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: NBC Ta Umarci Dukkan Tashoshin Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter

Sule yace: "Wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne, sun yi amfani da ranar da kasuwar ƙauyen ke ci, inda suka kai wannan mummunan harin kan mazauna garin."

"Munje wurin da lamarin ya faru, tawagar mu ta gudanar da bincike kan gawarwakin, wasu har an riga da an kaisu makwancin su."

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen ƙauyen sun tsere zuwa garuruwan dake kusa da su kamar kauyen Ogbaaulu.

Amma kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, bai daga kiran da aka masa ba, kuma bai amsa sakon da aka tura masa ba akan rahoton faruwar lamarin.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 26 a Wani Mummunan Hari a Jihar Zamfara

Wasu yan bindiga sun kai mummunan hari ƙauyukan jihar Zamfara, sun kashe akalla mutum 26.

Kakakin hukumar yan sanda na jihar, Shehu Muhammed, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel