Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 26 a Wani Mummunan Hari a Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 26 a Wani Mummunan Hari a Jihar Zamfara

- Wasu yan bindiga sun kai mummunan hari ƙauyukan jihar Zamfara, sun kashe akalla mutum 26

- Kakakin hukumar yan sanda na jihar, Shehu Muhammed, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar

- Yace yan bindigan sun sake yunkurin shiga wasu ƙauyakun amma jami'an yan sanda suka fatattake su

Yan bindiga sun kashe mutum 26 harda ɗan sanda a wani mummunan hari da suka kai wasu ƙauyukan dake yankin ƙaramar hukumar Bungudu, jihar Zamfara, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sace Wani Hakimi da Matansa 2 a Jihar Neja

Kakakin yan sandan jihar, Shehu Muhammed, ya bayyana cewa maharan ɗauke da manyan makamai sun kai hari ƙauyen Tofa, inda suka buɗe musu wuta suka kashe wasu daga cikin mutanen ƙauyen.

Shehu ya ƙara da cewa wasu yan bindigan suna kan hanyar su na kai wani hari a ƙauyen Samawa, amma sai jami'an yan sanda suka tare su, aka fara musayar wuta.

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 26 a Wani Mummunan Hari a Jihar Zamfara
Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 26 a Wani Mummunan Hari a Jihar Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace: "Wasu yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Tofa, inda suka fara harbi kan uwa da wabi, mazauna ƙauyen da dama sun rasa rayukansu a yayin harin."

"Yan bindigan sun kuma yi yunƙurin sake kai hari ƙauyen Samawa, amma jami'an yan sanda suka tare su aka fara musayar wuta."

"Maharan da dama sunji raunuka yayin fafatawar. Maharan sun sake komawa kauyen inda suka hana mazauna garin gudanar da jana'izar waɗanda aka kashe musu."

KARANTA ANAN: Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban Islamiyya da Yan Bindiga Suka Sace a Neja

A kwanan nan ne, wasu yan bindiga suka kashe manoma 12 tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki manoman ne suna tsakar aiki a cikin gonakinsu.

Lamarin ya faru ne a ƙauyukan Magami da Mayaba, ƙaramar hukumar Gusau, jihar Zamfara.

A wani labarin kuma Hatsari Ya Laƙume Rayukan Matasa 17 Akan Hanyar Dawowa Daga Ɗaurin Aure

Wasu matasan Kano guda 17 sun gamu da ajalinsu a wani hatsari da ya ritsa dasu akan hanyar Zariya zuwa Kano, kamar yadda dailynigerian ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun dawo ne daga ɗaura auren abokin su da suka halarta a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel