Da Ɗuminsa: Buhari Ya Naɗa Wa Mai Ɗakinsa, Aisha, Sabbin Hadimai Biyu

Da Ɗuminsa: Buhari Ya Naɗa Wa Mai Ɗakinsa, Aisha, Sabbin Hadimai Biyu

- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada wa mai dakinsa, Aisha, hadimai biyu

- Wadanda aka yi wa nadin sune Rukayyatu Gurin da Dakta Mohammed Abdurrahman

- Mutanen biyu da aka yi wa nadin sunyi karatun digirinsu na farko daga Jami'ar Maiduguri

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Rukayyatu Gurin a matsayin babban maitaimakawa na musamman kan mulki da harkokin mata a ofishin First Lady, The Punch ta ruwaito.

Mashawarcin shugaban kasa na musamman kan watsa labarai, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Da Duminsa: Buhari Ya Nada Wa Aisha Sabbin Hadimai Biyu
Da Duminsa: Buhari Ya Nada Wa Aisha Sabbin Hadimai Biyu. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Hukumar Yan Sanda Ta Dakatar Da Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu

A cewar sanarwar, Gurin tana da digirin digirgir daga Jami'ar Maiduguri sannan ta yi aiki a matsayin malama a Jami'ar ta Maiduguri, ta kuma rike wasu mukamai da suka hada da Mataimakin Direkta a Hukumar Kula da Jami'o'i, NUC, Direkta a Makarantar koyar dabarun mulki da tsare-tare, Kuru, babban malama a Jami'ar Baze da ke Abuja.

Ta maye gurbin Dr Hajo Sani wacce a baya bayan aka nada ta matsayin wakiliyar Nigeria a Kwamitin Ilimi da kimiyya na Majalisar Dinkin Duniya a Faransa.

Har wa yau, Buhari ya amince da nadin Dr Mohammed Abdurrahman a matsayin babban mashawarci na musamman ga Shugaban kasa kan Lafiya da abokan huldar cigaba a ofishin First Lady.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ɗan Kasuwa a Kano

Abdurrahman yana da digiri a fannin likitanci daga Jami'ar Maiduguri. Ya yi aiki a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri, Asibitin Kwararru na Yola, Cibiyar Lafiya ta Sithobela da ke Swaziland, Cibiyar Yaki da cutar Kanjamau sannan shine likitan First Lady daga 2015 zuwa 2019.

Zai cigaba da zama likitan First Lady duk da sabon nadin da aka yi masa.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Online view pixel