Bidiyon dan Najeriya mazaunin Turai: Zan dawo da tankar yaki na shiga Sambisa

Bidiyon dan Najeriya mazaunin Turai: Zan dawo da tankar yaki na shiga Sambisa

- Wani dan Najeriya da ke kasar waje ya sha alwashin dawowa gida dauke da tankar yaki don kare kasar daga ‘yan ta'adda

- Mutumin ya bayyana cewa, nan da makwanni hudu zai shiga da tankar yakin Najeriya don fara aikinsa na gyaran kasa

- A cewarsa, zai tuka tankara yakin zuwa dajin Sambisa da kansa da zaran ya iso Najeriya nan ba da jimawa ba

Wani dan Najeriya da ke zaune a kasar waje ya yi ikirarin cewa wani mutumin kirki ya bayar da gudummawar tankar yaki don yaki da rashin tsaro a kasar.

A wani bidiyo da @lindaikejiblogofficial ta wallafa a shafin Instagram, mutumin da ba a san ko wanene ba ya ce zai kawo tankokin yakin ne zuwa Najeriya inda zai yi amfani dasu wajen yakar mayakan Boko Haram, 'yan bindiga, IPOB da ESN.

A cewarsa, tankar yakin din zata iso Najeriya nan da mako hudu. Ya ce zai tantance ta a tashar jirgin ruwa ta Tin Can a yankin Apapa da ke Legas.

KU KARANTA: An sanar da mataki na gaba a shirin N-Power na gwamnatin Buhari

Bidiyon dan Najeriya mazaunin Turai: Zan dawo da tankar yaki na shiga Sambisa
Bidiyon dan Najeriya mazaunin Turai: Zan dawo da tankar yaki na shiga Sambisa Hoto: @lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

A kalamansa:

"Zai zama wuta ga wuta. Zan gama ku duka. Gaskiya na fusata kwarai da gaske."

'Yan Najeriya a shafin Instagram sun kasa daina dariya bisa lura cewa mutumin kawai wasa yake kuma bai kamata a saurareshi ba.

@legasha ya ce:

"Lmao. Zai kashe ni da dariya."

@ motayo41 yayi tsokaci:

"Ba na son yin magana amma mutumin abin dariya ne."

@ kic_ky4 ya rubuta:

"Na yarda da kai yallabai, za ka iya yin haka tunda Sojojin ba sa son yin aikinsu."

@ stalingrad326 ya ce:

"Ahhhh mutanen kauye sun same shi, iyalansa don Allah ku taimaka masa."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya shiga matukar jimamin mutuwar TB Joshua

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta yi gargadin cewa mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB na ganawa a wasu sassan jihar Edo don yada burinsu na ballewa a fadin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda da ke kula da aikin dawo da zaman lafiya a yankin Kudu-maso-Kudu, Moses Jitoboh, ya bayyana haka ne a jiya Laraba a lokacin kaddamar da aikin a Garin Benin.

Ya ce a yanzu haka ‘yan kungiyar IPOB suna gudanar da taron sirri a Igbanke, Ubiaja, Iguelaba, Igueben, Okhiahe da Ologbo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel