Ku kula, 'yan ta'addan IPOB sun shiga jihar Edo, suna shirya barna, in ji DIG
- 'Yan sanda sun gargadi mutanen yankin kudu maso kudu kan cewa su kula da barnar dake dumfaro su
- 'Yan sanda sun ce sun samu labarin akwai wuraren da 'yan IPOB ke shirya barna a wasu sassan jihar Edo
- Sun shawarci jama'ar jihar da su guji mummunan akidar ballewa irin ta 'yan ta'addan kungiyar IPOB a jihar
Rundunar ‘yan sanda ta yi gargadin cewa mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB na ganawa a wasu sassan jihar Edo don yada burinsu na ballewa a fadin jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda da ke kula da aikin dawo da zaman lafiya a yankin Kudu-maso-Kudu, Moses Jitoboh, ya bayyana haka ne a jiya Laraba a lokacin kaddamar da aikin a Garin Benin.
Ya ce a yanzu haka ‘yan kungiyar IPOB suna gudanar da taron sirri a Igbanke, Ubiaja, Iguelaba, Igueben, Okhiahe da Ologbo.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Afkawa Bankuna Da Ofishin 'Yan Sanda, Sun Yi Barna Sun Tsere
Ya shawarci al'ummomin yankin kan cewa su bijirewa wannan mummunan ra'ayin na 'yan kungiyar IPOB.
“An sanar da mu cewa akwai wasu wurare da masu neman ballewar kasar Ibo ke haduwa don haifar da rikici a jihar. Zai yi mana kyau a ce mutanen yankin su samar da bayanai masu amfani game da su.
A kan kiran da masu ruwa da tsaki suka yi wa mambobin kungiyar 'yan banga a jihar, DIG ya bukaci Kwamishinan 'yan sanda na jihar da ya yi aiki tare da shugaban kungiyar don kawar da baragurbi.
The Nation ta ruwaito DIG yana bayyana lura da cewa Edo da Bayelsa ne kadai jihohin da a yanzu suke cikin kwanciyar hankali a Najeriya, DIG ya shawarci mazauna yankin kudu maso kudu da kar su bar kungiyar IPOB ta yada akidar ballewa a yankin, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Limamin Ka'aba Ya Ziyarci Zulum, Ya Bayyana Irin Yadda Yake Ji Da Zulum
A wani labarin, Wani rahoto na musamman da jaridar The Cable ta fitar ta yi ikirarin cewa an gargadi Ahmed Gulak, sanannen jigo a jam’iyyar APC kan yin tafiya zuwa jihar Imo inda daga karshe aka harbe shi.
Jaridar, ta ambato wata majiya, da ta bayyana cewa Gulak ya yanke shawarar zuwa Owerri, babban birnin jihar Imo, domin jin ra’ayoyin jama’a game da sake duba kundin tsarin mulki, duk da gargadin da aka yi masa.
An ce marigayi dan siyasar ya dage kan tafiyarsa, yana mai cewa dukkanmu 'yan Najeriya ne.
Asali: Legit.ng