An sanar da mataki na gaba a shirin N-Power na gwamnatin Buhari

An sanar da mataki na gaba a shirin N-Power na gwamnatin Buhari

- Ma'aikatar Aikin jin kai ta kasa ta bayyana mataki na gaba a karkashin shirin N-Power da take dauka

- Ta ce tana shawartar wadanda aka zaba da su gaggauta hawa shafin hukumar don tabbatar da bayanansu

- Hakazalika an bada lambobin wayan da za a kira idan ma watakila an samu matsala wajen tabbatarwar

Ma'aikatar Aikin Jin Kai da Ci Gaban Jama'a ta sanar da mataki na gaba ga masu neman shiga shirin N-Power karkashin Batch C Stream One.

Babban Sakatare, Bashir Alkali, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi ya ce ma’aikatar ta fara mataki na gaba na yin rajista tare da tabbatar da adiresoshin imel ta masu neman shiga shirin.

Alkali ya yi kira ga wadanda aka zaba da su duba asusun sakonnin adiresoshin imail din su don tabbatarwa da samun karin bayani, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Dillalan albasa za su katse kai kaya zuwa Kudancin Najeriya daga ranar Litinin

An sanar da mataki na gaba a shirin N-Power na gwamnatin Buhari
An sanar da mataki na gaba a shirin N-Power na gwamnatin Buhari Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya kuma umarci masu neman shiga shirin da su shiga cikin shafin www.nasims.gov.ng don yin rajistar bayanan su tare da dangwalen yatsa.

Hakazalika ya kuma shawarci masu neman karin bayani su tuntubi layin taimakon N-Power a 018888340 ko 018888189 ko kuma imel don tallafi a support.npower@nasims.gov.ng don amsa musu tambayoyinsu.

Wannan shine karo na uku a daukar ma'aikatan wucin gadi a karkashin shirin na N-Power.

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya ta ce an biya dukkan kudaden da ya kamata a biya na wadanda suka amfana da N-Power na baya.

KU KARANTA: Lamarin Najeriya sai Allah, ku mika kukanku gareshi Obasanjo ga 'yan Najeriya

A wani labarin, Wani gwarzon bera da aka yi bikin saboda iya binciken nakiyoyin da aka binne ya kusa shiga wani ritayar da ta cancanta.

Beran mai suna Magawa haifaffen Tanzania yana da tarihin aiki na tsawon shekaru biyar wanda ya kai ga ceton rayukan maza da mata, da yara da manya wadanda barkewar abubuwan fashewa da ragowar yaki ya shafa.

Wata kungiyar kasar Belgium mai suna Apopo ce ta horas da beran mai shekara bakwai, wanda dan asalin kasar Tanzaniya ne kuma tana horas da dabbobi domin gano abubuwan fashewa da aka binne a karkashin kasa da kuma masu dauke da cutar tarin fuka a shekarun 1990.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.