Jirgin Sama Ya Makale A Cikin Laka Yayinda yake shirin tashi, Jami'ai Sun Yi Amfani Da Shebur Don Zakulo Shi

Jirgin Sama Ya Makale A Cikin Laka Yayinda yake shirin tashi, Jami'ai Sun Yi Amfani Da Shebur Don Zakulo Shi

- Wani bidiyon da ke nuna wasu jami’ai suna tono laka bayan jirgin saman Habasha ya makale a cikin lakar ya bazu a shafukan sada zumunta

- A cewar wani ganau, jirgin ya zame daga kan titin sannan ya makale a cikin laka yayin da matukin jirgin ke shirin tashi

- Wani mai amfani da Facebook mai suna Ayo Ojeniyi ne ya yada bidiyon a shafinsa, inda ya ce fasinjojin da matukan jirgin ba su samu rauni ba

Wani bidiyo ya yadu a shafukan sada zumunta inda aka ga wasu jami'ai suna share laka bayan jirgin Habasha ya makale a ciki.

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Ayo Ojeniyi wanda ya yada bidiyon a shafinsa ya ce babu abin da ya faru ga fasinjojin da ma’aikatan jirgin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Najeriya ta ba da umarnin hukunta wadanda suka karya dokar hana Twitter

Jirgin Sama Ya Makale A Cikin Laka Yayinda yake shirin tashi, Jami'ai Sun Yi Amfani Da Shebur Don Zakulo Shi
Jirgin Sama Ya Makale A Cikin Laka Yayinda yake shirin tashi, Jami'ai Sun Yi Amfani Da Shebur Don Zakulo Shi Hoto: Ayo Ojeniyi
Asali: Facebook

A cewarsa, wani dan jaridar kasa ne ya aiko masa da bidiyon. Da yake wallafa bidiyon a shafin sa, Ayo ya rubuta:

"Daga akwatin saƙo na / ɗan jaridar ƙasa: Jirgin saman Habasha yayin da yake shirin tashi ya zame daga kan titin sannan ya makale a cikin laka. Babu abin da ya faru da ma'aikatan da fasinjojin jirgin !!!

KU KARANTA KUMA: Na Sayi Wannan Keken Shekaru 40 Da Suka Wuce Akan N23 Kuma Zan Tuka Shi Har Mutuwa Na: Mutumin Kano

"Allah ya ci gaba da kare mu. Amin !!!"

Mutane da yawa suna magana kan bidiyon

Da yake mai da martani, Lexy Pexy a Facebook ya ce:

"Shin matukin jirgin yana bacci ne ko ya shagala? Muna bukatar sani"

Salam Timmy ya yi tsokaci:

"Mai yiwuwa an sami tsaiko ko kuma cunkoson ababen hawa kuma ya yi kokarin daukar wani bangare kamar yadda Micran Ibadan ke yi."

Odeyemi Oluwole ya ce:

"Wannan abin dariya ne sosai. Ina jin matukin jirgin ya shagala ne. Amma fa dukkanmu mutane ne, muna mantuwa wani lokacin. Ka yi tunanin amfani da shebur don fitar da 747."

A gefe guda, ‘Yan sanda a Jihar Kebbi sun ce ‘yan bindiga sun kashe mutum 66 a karamar Hukumar Danko-Wasagu da ke Jihar Kebbi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya ce kisan gillar ya faru ne a ranar Alhamis a kauyuka takwas na karamar hukumar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, duk da cewa rundunar na ci gaba da kirga yawan wadanda suka mutu, amma tuni hukumar 'yan sanda ta jihar ta aike da wasu jami'anta zuwa yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel