Yanzu Yanzu: Najeriya ta ba da umarnin hukunta wadanda suka karya dokar hana Twitter

Yanzu Yanzu: Najeriya ta ba da umarnin hukunta wadanda suka karya dokar hana Twitter

- Gwamnatin Najeriya ta bakin Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ta bayar da umarnin hukunta wadanda suka karya dokar hana Twitter a kasar

- Mai magana da yawun Malami, Umar Gwandu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, 5 ga watan Yuni

- Malami ya ba ofishin Daraktan Gurfanar da Jama’a na Tarayya da ya hanzarta hukunta wadanda suka karya umarnin Gwamnatin

Babban Atoni-Janar na tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni, ya umarci Daraktan Gurfanar da Jama’a na Tarayya da ya hanzarta hukunta wadanda suka karya umarnin Gwamnatin Tarayya na dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya.

Mai magana da yawun Malami, Umar Gwandu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken, ‘hana Twitter: Malami ya ba da umarnin gurfanar da masu laifin', jaridun Punch da Daily Nigerian suka ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya Ya Aika Sako Ga Buhari, Ya Bayyana Dalilai 5 Da Zai Sa A Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Twitter

Yanzu Yanzu: Najeriya ta ba da umarnin hukunta wadanda suka karya dokar hana Twitter
Yanzu Yanzu: Najeriya ta ba da umarnin hukunta wadanda suka karya dokar hana Twitter Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Sanarwar ta AGF ta ce:

“Babban Atoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN ya bayar da umarnin a gaggauta gurfanar da wadanda suka karya dokar Gwamnatin Tarayya kan ayyukan Twitter a Najeriya.
“Malami ya umarci Daraktan gurfanar da Jama’a na Tarayya na Ofishin Atoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, da ya fara aiki tukuru wajen hukunta wadanda suka karya dokar Gwamnatin Tarayya na dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya.
"Malami ya umarci DPPF da ya hada kai da Ma'aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Hukumar Sadarwa ta Kasa da sauran hukumomin gwamnati da suka dace don tabbatar da saurin hukunta masu laifin ba tare da wani bata lokaci ba."

KU KARANTA KUMA: Da dumi: 'Yan bindiga sun kashe mutane 66 a sabon harin da suka kai a kauyuka 8 na Kebbi

Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter

A wani labarin, tsohon sanata daga yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana wata hanya mafi sauki ga mutanen da ke son hawa shafin Twitter duk da hanin da aka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan kafar sada zumunta ta Twitter bisa goge wani rubutu da shugaban kasar ya yi, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Shawarar da Shehu Sani ya bayar, ta tsaya ne kan 'yan Najeriya dake rayuwa a jihar Legas, da kuma duk wadanda ke rayuWa a jihohin dake kusa da iyakokin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel