Yanzu-Yanzu: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Nada Sabon Shugaban Riko
- Hukumar jarrabawa ta NECO ta sanar da nadin sabon shugabanta na riko biyo bayan mutuwar tsohon shugaban
- A makon nan ne aka wayi gari da labarin mutuwar shugaban hukumar NECO, Godswill Obioma a jihar Neja
- Hukumar ta bayyana sabon nadin ne tare da jaddada ci gaban hukumar na aiki tukuru kamar yadda ta saba
Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta nada Mista Ebikibina John Ogborodi a matsayin mukaddashin Shugaban zartarwa na hukumar.
Wannan ya biyo bayan mutuwar Farfesa Godswill Obioma a ranar 1 ga Yuni, 2021, Daily Trust ta ruwaito.
Har zuwa lokacin nadin nasa, Mista Ogborodi ya kasance Daraktan Ayyuka na Musamman a hukumar.
A cikin wata sanarwa, Daraktan, Gudanar da Daukan Ayyuka, Mista Mustapha K. Abdul, ya bayyana cewa Kwamitin Gudanarwar ya amince da nadin Mukaddashin Shugaban a taron gaggawa da ta gudanar a ranar 2 ga Yuni, 2021.
KU KARANTA: Ni Zan Rera Wakar Taken Kasa Idan Aka Sauyawa Najeriya Suna, Inji Naira Marley
“Sanarwar ta bayyana cewa nadin Mista Ogborodi ya kasance ne sakamakon kasancewarsa Babban Darakta a Majalisar. Ta ce dukkanin ayyukan majalisar za su ci gaba ba kakkautawa kamar yadda aka tsara tun farko,” in ji shi.
Mista Ogborodi ya fito ne daga karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa.
Ya yi Digiri na farko a Jami’ar Jos a 1986 da kuma Digiri na biyu a wannan jami’ar a 1999.
Sabon shugaban ya shiga aikin NECO a 1999 kuma ya yi aiki a wurare daban-daban.
Ya kasance tsohon mukaddashin Darakta, Sashin Bunkasa Jarabawa; Mukaddashin Darakta, Ofishin Shugaba; Darakta, Janar na Ayyuka, Gudanar da Daukar Aiki da sauransu.
Ogborodi yayi aure kuma Allah ya albarkace shi da yara.
KU KARANTA: Babu Hadi: Lai Mohammed Ya Caccaki Masu Kwatanta Sheikh Gumi da Nnamdi Kanu
A wani labarin, A yau Talata ne aka wayi gari da labarin mutuwar shugaban hukumar jarrabawa ta NECO, wanda aka ce wasu ne suka kashe shi, jaridar Punch ta ruwaito.
Sai dai, majiyoyi masu karfi daga garin Minna a jihar Neja sun yi watsi da rahotannin da ke cewa an kashe Farfesa Godswill Obioma, shugaban na Hukumar Kula da Jarabawa ta Kasa (NECO).
A wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samo daga hukumar, NECO tace Obioma ya mutu ne kawai sabanin yadda aka ce wai an kashe shi.
Asali: Legit.ng