Ra'ayoyin 'Yan Kasa Kan Kudurin Sauyawa Najeriya Suna 'United African Republic'

Ra'ayoyin 'Yan Kasa Kan Kudurin Sauyawa Najeriya Suna 'United African Republic'

- Bayan ba da shawarin sauyawa Najeriya suna, wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu

- Wasu sun dauki lamarin da zafi, wasu kuwa sun dauke shi a matsayin raha kuma abin dariya

- Legit ta tattaro wasu daga cikin sharhin 'yan Najeriya daga shafin Twitter kan kudurin sauyin

A yau ne aka tashi da labarin da ya jawo cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya, inda kowa yake tofa albarkacin bakinsa a matsayin dan kasa mai kishi.

An bada shawarin sauyawa Najeriya suna zuwa Hadaddiyar Janhuriyar Afrika wacce turance take nufin 'United African Republic' a takaice kuwa, UAR.

Wasu shahararren 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da shawarin sauyin, wanda Legit.ng Hausa ta tattarowa mabiyanta.

KU KARANTA: Ya kamata Twitter ta bar Najeriya: Adamu Garba ya caccaki Twitter saboda Buhari

Ra'ayoyin 'Yan Kasa Kan Kudurin Sauyawa Najeriya Suna 'United African Republic'
Ra'ayoyin 'Yan Kasa Kan Kudurin Sauyawa Najeriya Suna 'United African Republic' Hoto: dailypost.ng
Asali: Depositphotos

@ShehuSani ya ce:

"Sunan Ghana ya samo asali ne daga tsohuwar Daular Afirka wacce ba ta taba faduwa zuwa yankin Ghana na yanzu ba. Canza suna bai zama dole ba amma idan ya zama dole mu canza, ya zama mun koma Jamhuriyar SONGHAI; tsohuwar daular Songhai ta fadada har zuwa sassan Najeriya na yanzu."

@EvansTed101 ya rubuta, tare da lika hoton samfurin kudi:

"A yanzu ni ne sabon kudin ga Hadaddiyar Jamhuriyar Afirka. Mutane za ku ga shegantaka!"

@frankdonga_ ya ce:

"Ku tsaya, idan muka canza sunanmu zuwa Hadaddiyar Jamhuriyar Afirka, me zai faru da jollof din Najeriya?"

@hiseth

"Idan ana kiran mutane daga Najeriya 'yan Najeriya, menene za a kira mutanen Hadaddiyar Jamhuriyar Afirka?"

Haka dai aka dinga samun sharhi daga 'yan Najeriya barkatai, wasu sun dauka da zafi, wasu kuwa a raha suka dauki wannan shawari na sauyin suna.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Nada Sabon Shugaban Riko

A wani labarin, Shahararren mawaki, Naira Marley ya bayyana cewa zai yi zaman jira don rera sabuwar wakar taken kasa bayan yanke shawarar sauya sunan Najeriya zuwa Hadaddiyyar Jamhuriyar Afirka (UAR).

A cewar rahotanni, Adeleye Jokotoye, kwararre kan haraji, ya gabatar da shawarar ga kwamitin a taron sauraron kararrakin yankin Kudu maso Yamma da ke Legas a ranar Laraba, 2 ga Yuni, 2021, jaridar Pulse ta ruwaito.

Yayin da yake gabatar da wannan shawara, ya ce sunan Najeriya turawan mulkin mallaka ne suka tilastawa kasar kuma ya kamata a canza shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel