Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar ‘yan sanda

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar ‘yan sanda

- Shugaba Muhammadu Buhari na shugabantar zaman majalisar 'yan sanda a fadar shugaban kasa da ke Abuja

- Taron ya samu halartan mataimakin shugaban kasa, shugaban kungiyar gwamnonin kasar da manyan jami'an gwamnati

- Har ila yau an ga mukaddashin Sufeto-Janar na 'yan sanda, Usman Baba a wurin taron amma ba ya cikin tattaunawar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar ‘yan sanda a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, jaridar The Nation da Daily Nigerian suka ruwaito.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo; Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

KU KARANTA KUMA: Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar ‘yan sanda
Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar ‘yan sanda Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Sauran wadanda ke halartar taron a zahiri su ne Shugaban Ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi; Ciki, Ra’uf Aregbesola; Babban Birnin Tarayya (FCT) Muhammed Bello da Shugaban Hukumar Kula da ’Yan sanda (PSC), Musiliu Smith.

An kuma ga mukaddashin Sufeto-Janar na 'yan sanda, Usman Baba a wurin taron amma ba ya cikin tattaunawar.

Akwai tsammanin Majalisar na iya tabbatar da nadin mukaddashin Shugaban ‘yan sandan.

Buhari a ranar 6 ga Afrilu ya nada Usman Baba a matsayin mukaddashin Sufeto Janar na 'yan sanda.

Ganawar, wacce aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis 27 ga Mayu, 2021, an dage ta ne don girmama marigayi Babban hafsan sojan, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu Manyan hafsoshin Soja da Ma’aikata 10, wadanda suka mutu a hatsarin jirgin sama.

KU KARANTA KUMA: Gumi ga FG: Ku sasanta da yan bindigar da suka tuba, ku yi amfani da su wajen yakar wadanda suka ki saduda

A wani labarin, mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin sadarwa na zamani, ya kula surutan da ake yi a kan cewa ana wani yunkuri na sake wa kasar nan suna.

Bashir Ahmaad ya tabbatar da cewa babu ruwan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ‘yan majalisar wakilan tarayya da wannan kudirin.

Hadimin na shugaba Muhammadu Buhari yace wani mutum ne a karon kansa ko a karkashin wata kungiya ya gabatar da wannan kudiri a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel