Hadimin Buhari ya yi magana a game da shirin canzawa Najeriya suna zuwa UAR a Majalisa

Hadimin Buhari ya yi magana a game da shirin canzawa Najeriya suna zuwa UAR a Majalisa

- Fadar Shugaban kasa ta ce babu hannunta a neman canza sunan Najeriya

- Bashir Ahmad ya yi magana a Twitter, ya ce wani ne ya kai wannan kudiri

- Mai ba Shugaban Najeriyar shawara yake cewa ba da hannun gwamnati ba

Mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin sadarwa na zamani, ya kula surutan da ake yi a kan cewa ana wani yunkuri na sake wa kasar nan suna.

Bashir Ahmaad ya tabbatar da cewa babu ruwan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ‘yan majalisar wakilan tarayya da wannan kudirin.

Hadimin na shugaba Muhammadu Buhari yace wani mutum ne a karon kansa ko a karkashin wata kungiya ya gabatar da wannan kudiri a ranar Laraba.

KU KARANTA: IPOB sun jawo ‘Yan kasuwan Kano sun yi asarar Miliyoyi

A cewar Bashir Ahmaad, ba shugaban kasa ba ne ko gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan majalisar wakilai su canza sunan kasar zuwa United Africa Republic.

Da yake magana a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, 2021, ya yi wannan karin-haske.

Ahmaad yake cewa wasu mutane sun dauki lamarin sun sa a kai, har suna zargin Mai girma shugaba Muhammadu Buhari da neman sakewa Najeriya suna.

"Ba gwamnatin Najeriya, musamman shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin canza suna ba, wani mutum ne ko kungiya suka nemi hakan."

KU KARANTA: Ana so Najeriya ta koma 'United African Republic

Hadimin Buhari ya yi magana a game da shirin canzawa Najeriya suna zuwa UAR a Majalisa
Shugaban kasa Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

"Amma wasu da-dama sun fara daukar maganar a kai, suna zargin shugaban kasar da yin abin da babu hannunsa gaba daya a ciki.” Inji Bashir Ahmaad.

Da yake magana game da lamarin, Shehu Sani ya ce idan har za a canzawa kasar nan suna, sai a zaba mata SONGHAI, a maimakon a kira ta kasar UAE.

Tsohon Sanatan ya tabo tarihi, ya ce tsohuwar Daular SONGHAI da aka kafa, ta shigo har Najeriya.

A jiya ne kuma aka ji cewa wasu kungiyoyin Arewa sun fito suna cewa gwamnatin tarayya ba mutanen Biyafara ‘yancin-kansu domin kasar nan ta zauna lafiya.

CNG ta ce kwanciyar hankali da zaman lafiya shi ne a hakura a raba Najeriya biyu, ta yadda masu fafutukar Biyafara za su kafa kasar su ce mai cin gashin kanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel