'Yan bindiga 5 sun hadu da ajalinsu bayan sun yi arangama da 'yan sanda a Katsina

'Yan bindiga 5 sun hadu da ajalinsu bayan sun yi arangama da 'yan sanda a Katsina

- Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da sheke 'yan bindiga biyar a karamar hukumar Kurfi ta jihar

- An gano cewa a yammacin ranar Laraba ne 'yan bindigan da zasu kai dari da hamsin suka shiga kauyukan Wurma da Yarbudu

- 'Yan sandan sun toshe hanyar da 'yan bindiga zasu tsere ta Dutsin-ma inda suka sheke karin hudu har lahira

An tabbatar da kisan 'yan bindiga biyar a yammacin Laraba yayin da suka yi arangama da rundunar 'yan sanda a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan da zasu kai dari da hamsin sun tsinkayi kauyukan Wurma da Yarbudu, jaridar ThisDayLive ta ruwaito.

Amma kuma 'yan sandan dake kauyen Wurma sun yi gaba da gaba da 'yan bindigan. Majiya daga rundunar 'yan sandan tace daya daga cikin 'yan bindigan ya sheka lahira.

KU KARANTA: Twitter ta bayyana dalilin da yasa ta goge wallafar da shugaba Buhari yayi

'Yan bindiga 5 sun hadu da ajalinsu bayan sun yi arangama da 'yan sanda a Katsina
'Yan bindiga 5 sun hadu da ajalinsu bayan sun yi arangama da 'yan sanda a Katsina. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji sun sheke mayakan ISWAP, sun lalata musu motocin yaki 6 a Borno

Daga bisani an gano cewa wata rundunar 'yan sanda dake wurin Dutsin-Ma ta rufe hanyar da 'yan bindigan zasu bi a kauyen Yarbudu wanda ya janyo sabuwar arangama tsakanin 'yan sandan da 'yan bindiga.

'Yan bindiga hudu suka mutu a wannan rangamar yayin da sauran suka tsere cikin daji da miyagun raunika, The Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis.

Ya ce 'yan sanda sun samu kwace babura shida daga wadanda 'yan bindigan suka yi amfani dasu wurin kai harin.

A wani labari na daban, Mathew Hassan Kuka, babban limamim cocin katolika na jihar sokoto, ya jajanta yadda shugabannin siyasa ke rantsuwa da kuma yadda rashin tsaro ke hauhawa a kasar nan.

Ya bukaci 'yan siyasa da su daina daukan rantsuwar da ba zasu iya cikawa ba, HumAngle ta ruwaito.

Bishop Kuka ya sanar da hakan ne a Kaduna, ranar Talata, 1 ga watan Yunin 2021 yayin bikin birne marigayi Rabaren Alphonsus Yashim Bello, limamin cocin katolika na Katsina wanda 'yan ta'adda suka kashe a ranar Juma'a, 21 ga watan Mayun 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel