Da duminsa: Sojoji sun sheke mayakan ISWAP, sun lalata musu motocin yaki 6 a Borno

Da duminsa: Sojoji sun sheke mayakan ISWAP, sun lalata musu motocin yaki 6 a Borno

- Rahotanni masu dadi daga jihar Borno suna nuna manyan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu a yaki da ta'addanci

- An gano cewa dakarun sun sheke 'yan ta'adda masu tarin yawa kuma sun lalata a kalla motocin yakin 'yan ta'addan shida

- 'Yan ta'addan da ake zargin mayakan ISWAP ne sun shiga garin Damboa domin tada zaune tsaye amma sai suka tarar da ajalinsu

Dakarun sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram masu yawa tare da lalata motoci shida na yakin 'yan ta'addan a ranar Laraba, 2 ga watan Yuni.

Kamar yadda PR Nigeria ta ruwaito, an kashe 'yan ta'addan masu yawa bayan musayar ruwan wuta da sojojin a garin Damboa a jihar Borno.

KU KARANTA: JTF ta kama mutum 10 da ake zargi da kisan jami'an tsaro a Akwa Ibom, an samu miyagun makamai

Da duminsa: Sojoji sun sheke mayakan ISWAP, sun lalata musu motocin yaki 6 a Borno
Da duminsa: Sojoji sun sheke mayakan ISWAP, sun lalata musu motocin yaki 6 a Borno. Hoto daga @TVCNews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Har yanzu gwamnati bata tuntubemu ba, Hukumar makarantar da aka sace yara 156

Kamar yadda TVCNews ta wallafa, majiyar tsaro mai karfi ta bayyana cewa wasu mayakan Boko Haram din sun tsere da miyagun raunika da aka yi musu da harbin bindiga.

Kamar yadda majiyar tace, 'yan ta'addan sun kutsa Damboa a motocin yaki 11 inda suka yi yunkurin kutsawa sansanin sojoji. Sun kutsa cikin farar hula amma sai sojojin suka fi karfinsu.

Legit.ng ta tattaro cewa lamarin ya tada hankulan mazauna yankin inda suka dinga gudun ceton rayukansu.

A halin yanzu, an tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya koma yankin bayan nasarar da zakakuran sojojin suka samu.

A wani labari na daban, 'yan bindiga da ake zargin mayakan ISWAP ne a halin yanzu suna kai farmaki sansanin sojoji dake yankin kudancin Borno, kamar yadda majiyoyin tsaro suka sanar.

Kungiyar miyagun 'yan ta'addan sun tsinkayi garin Damboa wurin karfe 10:30 na safe da motocin yaki masu yawa, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya saka jama'ar garin cikin dimuwa yayin da mazauna garin da 'yan gudun hijira ke gudun ceton rayukansu.

Kamar yadda majiyar tace, tuni dakarun sojin sama suka garzaya ta jiragen yaki domin baiwa sojojin da 'yan sa kai taimako.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel