Twitter ta bayyana dalilin da yasa ta goge wallafar da shugaba Buhari yayi

Twitter ta bayyana dalilin da yasa ta goge wallafar da shugaba Buhari yayi

- Twitter ta bayyana dalilin da yasa ta goge wallafar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a kafar

- Kamar yadda karin bayani ya nuna bayan goge wallafar, Twitter tace wallafar ta sabawa ka'idojinta

- Kafar sada zumuntar ta goge wallafar shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake jan kunnen 'yan ta'addan IPOB

Twitter ta yi bayanin dalilinta na goge wallafar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a kafar sada zumuntar, lamarin da ya kawo cece-kuce daga 'yan Najeriya.

Wallafar wacce take daga cikin wallafofin da Buhari yayi a ranar Talata ta ce: "Da yawa daga cikin masu rashin da'a a yau basu da wayon sanin asara da rashin rayuka da aka yi yayin yakin basasa.

"Mu da muke filin daga na watannin 30, muka ga yaki, za mu yi musu magana da yaren da muka san zasu gane."

KU KARANTA: Matawalle ya ba Zamfarawa wa'adin kwana 7 su mika makaman da suka mallaka

Twitter ta bayyana dalilin da yasa ta goge wallafar da shugaban Buhari yayi
Twitter ta bayyana dalilin da yasa ta goge wallafar da shugaban Buhari yayi. Hoto daga @TheCableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: ISWAP suna kai hari sansanin sojoji a jihar Borno, jama'a na gudun ceton rai

Tuni Twitter ta goge wallafar tare da maye gurbinta da "Wannan wallafar ta sabawa dokokin Twitter. Samu karin bayani."

Idan mai karatu kuwa ya latsa wurin samun bayanin, zai kai shi shafin da Twitter ta bayyana dalilinta na daukan wannan matakin.

Kamar yadda Twitter tace: "Idan muka gano cewa wallafa ta saba ka'idojinmu, mu kan bukaci mawallafin ya gogeta kafin ya iya sake wata wallafa.

"Mu na tura sako ta yanar gizo ga wanda ya saba ka'idar sannan mu sanar dashi kurensa da kuma dokar da ya saba.

“Daga nan ne za a fara batun goge wallafar ko kuma ya bukaci mu sake duba wallafar idan akwai kuskure."

A wani labari na daban, jami'an tsaron hadin guiwa (JTF) sun damke jama'a masu yawa masu alaka da kashe-kashen jami'an tsaro a kananan hukumomin Essien udim, Oboto Akara da Ikot Ekpene dake jihar Akwa Ibom.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, kamen ya biyo bayan jerin samamen da JTF din da suka hada sojoji, 'yan sanda, jami'an DSS da na NSCDC ke kaiwa wurare daban-daban da suka zama maboyar 'yan ta'adda a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Andrew Amiengheme, a wata takardar da ya fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa JTF din sun samo ababen hawa da makamai daga wadanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng