Babu Hadi: Lai Mohammed Ya Caccaki Masu Kwatanta Sheikh Gumi da Nnamdi Kanu

Babu Hadi: Lai Mohammed Ya Caccaki Masu Kwatanta Sheikh Gumi da Nnamdi Kanu

- Ministan yada labarai ya caccaki masu cewa gwamnati ta kame malamin addini Sheikh Gumi

- Ya kuma yi kaca-kaca da ikirarinsu na cewa Sheikh Gumi da Nnamdi Kanu matsayinsu daya

- Ya bayyana cewa, Kanu ya kasance yana jagorantar aikata ta'addanci kan jami'ian tsaron kasa

Lai Mohammed, ministan yada labarai, ya ce ayyukan da Ahmed Gumi, mashahurin malamin addinin Islama ya ke yi, ba za a iya kwatanta su da na Nnamdi Kanu ba, shugaban kungiyar da ke ikirarin ballewa daga kasa, The Cable ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin zantawarsa da manema labarai na fadar gwamnati a Abuja.

Mohammed yana amsa tambaya ne a kan dalilin da ya sa Gumi - wanda ya yi kira a yi afuwa ga ‘yan bindiga - gwamnatin tarayya ba ta bayyana cewa tana neman sa ruwa a jallo ba.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Motar Bas Ta Makaranta a Ondo

Babu Hadi: Lai Mohammed Ya Caccaki Masu Kwatanta Sheikh Gumi Nnamdi Kanu
Babu Hadi: Lai Mohammed Ya Caccaki Masu Kwatanta Sheikh Gumi Nnamdi Kanu Hoto: 1.bp.blogspot.com
Asali: UGC

Ministan, wanda ya lura cewa babu wanda ya nada Gumi a matsayin kakakin masu tayar da kayar baya, ya ce matsayin malamin ya bambanta da na Kanu, ya kara da cewa shugaban IPOB din ya fito fili ya yi kira da a kai hari kan jami'an tsaro.

Ya ce akwai mutane da yawa da ke “zuga kiyayya” ga Shugaba Muhamadu Buhari, ya kara da cewa da an kame irin wadannan mutanen, da an cika magarkama.

Lai Mohammed ya ce: "Amma abinda nake cewa kada ku kwatanta kowa da Kanu wanda karara ya ce, 'ku je ku kashe 'yan sanda.' Ina ganin wani lokaci... 'yan sanda 'yan uwa ne; su baffannin mu ne; su ma suna da yara.

“[Lokacin da aka kashe su], matansu sun zama zawarawa, 'ya’yansu sun zama marayu. Kuma menene laifin wadannan ‘yan sanda? Saboda suna aiki don ganin kasar ta zama daya. Sojojin da suke saka rayukansu fa don ni da ku ku iya bacci fa?

"Ba abin yarda ba ne a ko'ina a duniya ga kowa, a ko'ina, ya kasance cikin kwanciyar hankali a duk inda yake kuma a yanzu ya ba da umarnin a je a kashe sojoji, a je a kashe 'yan sanda," CEO Africa ta nakalto.

KU KARANTA: Ku kula, 'yan ta'addan IPOB sun shiga jihar Edo, suna shirya barna, in ji DIG

A wani labarin, Wani tsohon hadimin Shugaba Buhari, kan lamuran Majalisa, Abdurrahman Sumaila, ya ce ‘yan Najeriya masu tunani ba za su jefa rayukansu cikin hadari ba don mara wa takarar duk wani dan siyasar Kudu maso Gabas da ke neman shugabancin kasar nan a 2023 ba.

Sumaila ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.

“Tare da wadannan munanan dabi’un da mutanen Kudu-maso-Gabas suka aikata, ta yaya 'yan Najeriya za su ba su amanar su shugabance mu?

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.