Jami'an Kwastam Sun Kwace Kayayyakin da Suka Kai Na Miliyan N28m a Arewa

Jami'an Kwastam Sun Kwace Kayayyakin da Suka Kai Na Miliyan N28m a Arewa

- Jami'an hukumar kwastam NCS a yankin arewa ta tsakiya sun cafke kayayyaki da zasu kai na miliyan N28m

- Shugaban tawagar jami'an kwastam na yankin, Comptroller Olusegun Peters, shine ya bayyana haka

- Daga cikin kayayyakin da suka kama akwai buhunan shinkafa, buhunan sikari, katan ɗin madara da sauransu

Rundunar jami'an hukumar kwastam dake kula da bodar yankin arewa ta tsakiya ta bayyana cewa ta ƙwace kayayyaki dake da lambar duty DPV, of N 28,203,700 da akayi safarar su zuwa cikin ƙasa, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3, Sun Ƙona Gidaje 4 da Motoci Biyu a Imo

Da yake jawabi ga manema labarai a Ilorin, mai kula da yankin, Comptroller Olusegun Peters, yace sun ƙwace kayan ne a tsakanin watan Afrilu zuwa Mayu a Operation 35 da suka fita.

Jami'an Kwastam Sun Kwace Kayayyakin da Suka Kai Na Miliyan N28m a Arewa
Jami'an Kwastam Sun Kwace Kayayyakin da Suka Kai Na Miliyan N28m a Arewa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yace: "Abubuwan da aka kama sun haɗa da buhunan shinkafa yar ƙasar waje 637, Galan dake cin lita 25 na man injin mota guda 15, ."

"Sauran kayayyakin sun haɗa da Katan ɗin madara guda 14, Katan ɗin batiri guda 4, Tumaturin gwangwani guda 14 da kuma buhunan sikari guda uku."

Yace jami'an tawagarsa sun sami wannan nasara ne saboda haɗin kan da suka samu daga NCS, ofishin mai bada shawara akan tsaro na ƙasa da sauran su.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya

"Wannan ya ƙara wa jami'an ƙwarin guiwa da jajircewa wajen aikin su a ko da yaushe. Duk da harin da masu safara da yan bindiga suke kaiwa jami'an, hakan baya hana su gudanar da aikin su," Inji shi.

A wani labarin kuma Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Yayi Magana Kan Shirinsa Na Sauya Sheƙa Zuwa APC Ranar 12 Ga Yuni

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya musanta rahoton cewa yana shirin komawa jam'iyyar APC ranar 12 ga watan Yuni.

Matawalle yace har yanzun bai yanke hukunci ko kuma ya sanya ranar da zai sauya sheƙa ba, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel