Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3, Sun Ƙona Gidaje 4 da Motoci Biyu a Imo

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3, Sun Ƙona Gidaje 4 da Motoci Biyu a Imo

- Wasu yan bindiga sun hallaka mutum uku tare da ƙona gidaje huɗu da motoci biyu a jihar Imo

- Wani daga cikin iyalan waɗanda aka kashe ne ya bayyana haka ga manema labarai kuma ya nemi a sakaya sunan sa

- Yace mutum uku aka kashe ba ɗaya ba kamar yadda mutane suke yaɗawa a kafafen sada zumunta

Wani bincike da jaridar Vanguard ta gudanar ya nuna cewa yan bindiga sun hallaka mutum uku ranar Litinin da daddare, daga cikinsu harda shugaban matasan PDP a Awonmama, ƙaramar hukumar Oru jihar Imo.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Wani daga cikin iyalan ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, shine ya bayyana haka ga manema labarai.

Ya roƙi jami'an tsaro su taimaka su binciko waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin na kisa.

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3, Sun Ƙona Gidaje 4 da Motoci Biyu a Imo
Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3, Sun Ƙona Gidaje 4 da Motoci Biyu a Imo Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Ya bayyana cewa ya kamata mutane su sani mutum uku aka kashe ba ɗaya ba kamar yadda ake yaɗawa.

KARANTA ANAN: Rahoto: Sama da Yan Najeriya 10,000 Sun Kamu da Rashin Lafiya Bayan an Musu Rigakafin COVID19 Kashi Na Farko

A cewarsa: "An kashe mana mutum uku a iyalan mu, Kenneth Amukaamara, shugaban matasan jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Oru ta gabas, Eugene Anyia Amukaamara da kuma Adaeze Anyia Amukaamara."

"Sun ƙona gidaje huɗu da kuma motoci biyu. Aikin jami'an tsaro ne su binciko waɗanda suka aikata haka, wannan ne kaɗai abinda zan iya cewa a yanzun."

A wani labarin kuma Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa

Bayan an biyasu miliyan N5m, yan bindiga sun nemi a basu burodi da lemun kwalba mai sanyi a matsayin fansa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ɗan uwan matashin da aka sace, Mashood Adebayo, shine ya bayyana irin halin da suka shiga domin kuɓutar da ɗan uwansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262