Gwamna Ya Sallami Ma’aikata 532 a Jiharsa, Yace Yanzun Aka Fara
- Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau, ya sallami ma'aikata sama da 532 a faɗin jiharsa
- Gwamnan yace ya ɗauki wannan matakin ne bayan gano ma'aikatan sun bada bayanan ƙarya
- Yace gwamnatinsa zata cigaba da ɗaukar irin waɗannan matakan akan duk wanda aka kama da makamancin wannan laifin
Gwamnan jihar Plateau, Simon Baƙo Lalong, ya sallami ma'aikata sama da 532 a jihar sa bayan ya gano akwai matsala a bayanan karatunsu.
KARANTA ANAN: Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Yayi Magana Kan Shirinsa Na Sauya Sheƙa Zuwa APC Ranar 12 Ga Yuni
Lalong yace gwamnatinsa a shirye take ta sallami duk wani ma'aikaci da aka gano yayi ƙarya a bayanan sa ko ya yaudari gwamnati da bayanan bogi, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Gwamnan yace: "Sama da ma'aikatan gwamnati 532 waɗanda aka gano sun bada bayanan ƙarya, Gwamnati ta cire su daga tsarin biyan albashin jihar bayan gudanar da bincike ta hanyar amfani da Lambar BVN."
Gwamna Lalong ya bayyana haka ne a wurin taro na musamman da aka shirya wa sakatarorin gwamnati a makarantar NIPSS dake Kuru.
KARANTA ANAN: Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa
Gwamnan yace yanzun aka fara kuma gwamnatinsa zata cigaba da irin wannan binciken, duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci.
A baya-bayan nan ne, gwamnan jihar Kaduna ya sallami ma'aikata da dama a jiharsa, wanda hakan ya jawo cece kuce har ƙungiyar kwadugo ta tsunduma yajin aiki
A cewar El-Rufa'i, gwamnatinsa ba zata iya cigaba da ƙarar da kuɗin shigarta a albashin ma'aikata kaɗai ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A wani labarin kuma Bamu da Kudirin Zarcewa a Kan Mulki, INEC Zata Gudanar da Zaɓen 2023, Shugaba Buhari
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa bata sha'awar zarcewa akan mulki.
Buhari yace zai yi duk me yuwuwa wajen ganin an gudanar da zaɓe a 2023 duk da matsalar tsaron da ƙasar ke ciki.
Asali: Legit.ng