Yanzu-Yanzu: An Kama Wadanda Ake Zargin Sun Kashe AIG Christopher Dega

Yanzu-Yanzu: An Kama Wadanda Ake Zargin Sun Kashe AIG Christopher Dega

- Yan sanda sun ce sun kama wasu mutane da suke zargi da kashe AIG Christopher Dega

- Rahotanni sun nuna cewa yan bindigan sun bi sahun hadimin na Ortom ne zuwa wani wurin cin abinci a Buruku, Jos, suka harbe shi

- Rundunar yan sandan ta nuna bakin cikinta bisa rasuwar AIG Dega tana mai cewa za ta cigaba da zurfafa bincike

Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Plateau ta ce ta kama wasu da ta ke zargin sune suka kashe AIG Christopher Dega (mai murabus), babban mashawarcin Gwamnan Benue, Samuel Ortom kan tsaro, The Punch ta ruwaito.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa an kashe hadimin gwamnan ne a Jos, babban birnin jihar Plateau.

Yanzu-Yanzu: An Kama Wadanda Ake Zargin Sun Kashe AIG Christopher Dega
Yanzu-Yanzu: An Kama Wadanda Ake Zargin Sun Kashe AIG Christopher Dega. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Plateau, Ubah Ogaba, ya tabbatar da afkuwar hakan a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: 'Yan bindigan da suka sace ƴan Islamiyya a Neja sun nemi a biya N110m kuɗin fansa

Sanarwar da ya fitar ta ce, "Rundunar yan sandan jihar Plateau ta samu labarin bakin ciki na rasuwar AIG Christopher Dega (mai murabus).

"A ranar 31/01/2021 misalin karfe 8.30 na dare, wasu yan bindiga da ba a riga an gano su ba sun bindige AIG Christpher Dega a wani wurin cin abinci a Bukuru, Jos.

"Daga binciken da aka fara a yanzu, akwai alamun an bi sahunsa ne aka bindige shi.

"Ya iso garin Jos daga Makurdi a ranar da ya rasu misalin karfe 7.30 na yamma.

"An kama wasu da ake zargi da kashe shi. A halin yanzu, ana cigaba da bincike."

KU KARANTA: 'Yan Bindigan Da Aka Fatattaka Daga Katsina Da Zamfara Ne Ke Addabar Ƴan Neja, Sanata Abdullahi

Ortom na daya daga cikin wadanda ke magana game da kashe-kashen da yan bindiga ke yi a sassan Nigeria. Gwamnan kuma baya goyon bayan kiwo a fili sannan ya saka dokar hana kiwo a fili a jiharsa.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel