'Yan bindigan da suka sace ƴan Islamiyya a Neja sun nemi a biya N110m kuɗin fansa

'Yan bindigan da suka sace ƴan Islamiyya a Neja sun nemi a biya N110m kuɗin fansa

- Yan bindiga da suka sace ɗalibai daga Islamiyya a Niger sun tuntubi shugaban makarantar

- Alhaji Abubakar Alhassan shugaban islamiyya ya ce yan bindiga sun nemi a biya su N110 kuɗin fansa

- Alhaji Alhassan ya ce ya sanar da gwamnatin jihar abin da yan bindigan suka sace amma ta ce ba za ta biya kuɗin fansa ba

- A bangaren ta, gwamnatin na jihar Niger ta ce jami'an tsaro na aiki tukuru don dawo da yaran amma ba za su biya kuɗin fansa ba

Ƴan bindiga da suka sace ɗaliban makarantar islamiyya ta Salihu Tanko da ke Tegina a jihar Niger sun tuntubi mahukunta makarantar.

Yan bindiga sun tuntubi shugaban makarantar, Alhaji Abubakar Alhassan misalin ƙarfe 4 na yammacin Litinin suka nemi ya biya N110m a matsayin kuɗin fansar dalibansa, The Nation ta ruwaito.

'Yan bindiga da suka sace ƴan Islamiyya a Neja sun nemi a biya N110m kuɗin fansa
'Yan bindiga da suka sace ƴan Islamiyya a Neja sun nemi a biya N110m kuɗin fansa. Hoto: @ChannelsTV
Asali: UGC

A hirar da aka yi da shi a wayar tarho, Alhassan ya ce ƴan bindigan sunyi ikirarin dalibai 156 suka sace.

A cewarsa, masu garkuwar sun yi barazanar cewa za su halaka yaran idan ba a biya kuɗin a ranar ba.

DUBA WANNAN: An Kashe Sufetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Shida a Ƙauyen Katsina

Alhassan ya ce an sanar da gwamnatin jihar abin da yan bindigan suka ce amma ta ce ba za ta biya kuɗin fansa ba.

ThisDay ta ruwaito cewa wasu mutane a garin sun fara tara kudin da nufin za su kaiwa ƴan bindigan.

A bangaren ta, gwamnatin jihar ta ce ta fara ɗaukan matakan ganin cewa an ceto yaran amma fa babu batun biyan kudin fansa.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labarai na Gwamna Abubakar Sani Bello, Mary Noel Berje, ya ce mataimakin gwamna Alhaji Ahmed Mohammed Ketso ya ce, "Gwamnati na bin sahun yan bindigan kuma ana ƙoƙarin gano su.

KU KARANTA: Sabon Salo: 'Yan fashi sun fara zuwa sata gidajen mutane da na'urar POS

"Har yanzu ba a tantance adadin daliban ba. Amma jami'an tsaro na yin duk kai yiwuwa don ceto su.

"Ba mu biyan kudin fansa ga masu garkuwa. Muna kokarin tattaunawa ne domin ganin yadda za mu dawo da yaran cikin lafiya."

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel