Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe AIG Christopher Dega a Jos
- Wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun bindige AIG Christopher Dega (mai murabus) har lahira a Jos, Jihar Plateau
- Rahotanni sun nuna cewa yan bindigan sun bi sahun hadimin na Ortom ne zuwa wani wurin cin abinci a Buruku, Jos, suka harbe shi
- Rundunar yan sandan ta nuna bakin cikinta bisa rasuwar AIG Dega tana mai cewa za ta cigaba da zurfafa bincike
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe mataimakin sufetan yan sanda, AIG, Christopher Dega (mai murabus) a birnin Jos, jihar Plateau kamar yadda TVC News ta ruwaito.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Plateau, Ubah Ogaba, ya tabbatar da afkuwar hakan a ranar Laraba 2 ga watan Yunin 2021.
Rahotanni sun ce an yi ta harbinsa da bindiga a kirjinsa ne har sai da jini ya yi ta zuba daga jikinsa ya kuma ce ga garin ku.
DUBA WANNAN: 'Yan bindigan da suka sace ƴan Islamiyya a Neja sun nemi a biya N110m kuɗin fansa
Dega babban mashawarci na musamman ne ga gwamnan jihar Benue Samuel Ortom. Kafin ya yi murabus ya taba rike mukamin kwamishinan yan sanda a jihohin Borno da Edo.
Marigayin ya fito ne daga karamar hukumar Katsina Ala a jihar Benue.
Daga bisani, Rundunar yan sanda a jihar Plateau ta ce ta yi nasarar kama wasu da ta zargin suna suka bindige, hadimin gwamnan Benue, AIG Christopher Dega a garin Jos, The Punch ta ruwaito.
"Rundunar yan sandan jihar Plateau ta samu labarin bakin ciki na rasuwar AIG Christopher Dega (mai murabus).
"A ranar 31/01/2021 misalin karfe 8.30 na dare, wasu yan bindiga da ba a riga an gano su ba sun bindige AIG Christpher Dega a wani wurin cin abinci a Bukuru, Jos.
"Daga binciken da aka fara a yanzu, akwai alamun an bi sahunsa ne aka bindige shi.
DUBA WANNAN: 'Yan Bindigan Da Aka Fatattaka Daga Katsina Da Zamfara Ne Ke Addabar Ƴan Neja, Sanata Abdullahi
"Ya iso garin Jos daga Makurdi a ranar da ya rasu misalin karfe 7.30 na yamma.
"An kama wasu da ake zargi da kashe shi. A halin yanzu, ana cigaba da bincike," a cewar sanarwar.
Yan sandan sun ce binciken da suka fara gudanarwa ya nuna cewa maharan sun yi ta bin sahun Dega ne har zuwa wani wurin cin abinci a Buruku inda suka bude masa wuta.
A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.
Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.
Asali: Legit.ng