Hukumar Kwastam Zata Fara Horad da Jami’an Kwastam Na Ƙasashen Waje Kan Yaƙi da Yan Ta’adda, Inji Hameed Ali
- Shugaban NCS, Hameed Ali, yayi alƙawarin cewa hukumar sa zata fara horad da jami'an kwastan na nahiyar Africa
- Mr. Ali yace za'a samar da wuri na musamman da zai ɗauki jami'ai da dama domin basu horo kan yaƙi da ta'addanci
- Shugaban ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙunci darakta janar na kwastam ɗin nahiyar Africa
Shugaban hukumar kwastam na ƙasa, Hameed Ali, ya bayyana shirin hukumar sa na fara horad da takwarorinsu na ƙasashen dake maƙwabtaka da Najeriya kan yadda zasu yaƙi ta'addanci da sauran ƙalubalen bakin boda.
KARANTA ANAN: Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Yayi Magana Kan Shirinsa Na Sauya Sheƙa Zuwa APC Ranar 12 Ga Yuni
Ya ƙara da cewa wannan na daga cikin bangaren NCS na aiki tare da sauran takwarorinta na ƙasashen nahiyar Africa, kamar yadda punch ta ruwaito.
Mr. Ali yace shirin zai ƙunshi buɗe wuri na musamman domin bada horo ga jami'an kwastam na sauran ƙasashen Africa.
Ali ya bayyana hakane a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Darakta Janar, na kwastan ɗin dake nahiyar Africa, Mr Fredrick Inamo, tare da tawagarsa.
Hameed Ali yace: "Muna shirin buɗe wuri na musamman da zai ɗauki jami'an kwastan daga ƙasashen Africa, su zo mu basu horo. Zamu sanar daku da zaran mun kammala shire-shirye."
"Zamu cigaba da taimaka wa juna da bayanai kan ayyukan ta'addanci da sauran ƙalubalen da muke fuskanta a bakin boda."
KARANTA ANAN: Gwamna Ya Sallami Ma’aikata 532 a Jiharsa, Yace Yanzun Aka Fara
"Yana da kyau mu rinƙa aiki tare domin taimaka wa juna. Zamu nuna muku yanayin aikin mu, ba zamu damu ba dan mun koya muku yadda muke aiki domin ƙara muku ƙwarin guiwa. Zamu tura muku jami'an mu idan buƙatar hakan ta taso."
Da yake tsokaci kan wannan dama da aka basu, Inamo yace haɗin guiwar da aka yi a baya ya fara haifar da ɗa mai ido.
A wani labarin kuma Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa
Bayan an biyasu miliyan N5m, yan bindiga sun nemi a basu burodi da lemun kwalba mai sanyi a matsayin fansa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Ɗan uwan matashin da aka sace, Mashood Adebayo, shine ya bayyana irin halin da suka shiga domin kuɓutar da ɗan uwansu.
Asali: Legit.ng