Kada ku siyasantar da kisan Gulak, gwamnonin arewa sun gargadi ‘yan Najeriya

Kada ku siyasantar da kisan Gulak, gwamnonin arewa sun gargadi ‘yan Najeriya

- Gwamnonin arewa sun yi Allah wadai da kisan Ahmed Gulak

- Hakanan, gwamnonin sun bukaci ‘yan Najeriya da kada su siyasantar da kisan Gulak

- A cewarsu, wannan na iya haifar da karin tashin hankali

An aika gagarumin sako ga 'yan Najeriya game da kisan Ahmed Gulak, wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ce ta aika sakon. Sakon ya ce: Kada a siyasantar da lamuran da ke kewaye da kisan Gulak, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: A ƙarshe dan Gulak ya magantu, ya bayyana kalmomin mahaifinsa na ƙarshe

Kada ku siyasantar da kisan Gulak, gwamnonin arewa sun gargadi ‘yan Najeriya
Kada ku siyasantar da kisan Gulak, gwamnonin arewa sun gargadi ‘yan Najeriya Hoto: @PoliceNG, @EbiXkapade
Asali: Twitter

A wata sanarwa a madadin gwamnonin arewa, shugaban kungiyar kuma gwamnan Filato, Simon Lalong, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma ta’addanci wanda dole ne a yi tir da shi.

Gwamnan ya yi gargadi game da sanya siyasa a cikin al'amuran da suka shafi mutuwar wanda ka iya haifar da wani tashin hankali.

Hakazalika yayinda yake martani kan kisa Gulak, Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya bayyana kisan nasa a matsayin babban laifi. Ya yi kira da a hanzarta gudanar da bincike domin gurfanar da duk wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban shari’a.

A cewar Lawan, babu wani hujja a kan kisan dan Adam da dan kasa, jaridar Thisday ta ruwaito.

Ku tuna cewa kamishinan yan sandan jihar Imo, Abutu Yaro, yace jami'an hukumar yan sanda sun gano waɗanda suka kashe Ahmed Gulak, fitaccen ɗan siya kuma jigo a APC, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

Kwamishinan ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya aike wa hukumar dillancin labarai (NAN) ɗauke da sanya hannun sa ranar Lahadi.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Zamfara ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar

Yace Jami'ai sun ɗauki matakin gaggawa bayan samun sahihin bayanai kan maharan, nan danan suka bi sawun su kuma suka gano su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel