Gwamnan Zamfara ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar

Gwamnan Zamfara ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar

- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya sauke dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar

- Gwamnan ya bukaci shugabannin hukumomi, ma'aikatu tare da duk mambobinsu da su mika ragamar mulkinsu ga manyan sakatarorinsu

- Kamar yadda yace, dukkan hukumomin da kundun tsarin mulki na kasa ya kafa a jihar zasu iya cigaba da ayyukansu

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa na jihar.

Kamar yadda takardar da mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Zailani Bappa ya fitar a ranar Litinin ta nuna, gwamnan ya bukaci dukkan kwamishinoni da masu mukaman siyasa na jihar da su koma gida su huta.

Kamar yadda wasikar da Zailani Bappa ya wallafa a shafinsa na Facebook ta bayyana, gwamnan yace wannan sallamar bata shafi duk wata hukumar da kundun tsarin mulkin kasar Najeriya ya kafa ba a jihar.

KU KARANTA: Abu mai Fashewa ya Tashi da Sojojin Najeriya, 7 sun Sheka Lahira a Borno

Gwamnan Zamfara ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar
Gwamnan Zamfara ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

"Dr Bello Mohammed, Matawallen Maradun, Barden Hausa kuma Shettiman Sakkwato a yau 31 ga watan Mayun 2021 ya rushe majalisar zartarwa ta jihar.

"Sakataren gwamnatin jihar, shugaban ma'aikata da mataimakin shugaban ma'aikatan jihar tare da shugabanni da mambobin hukumomin jihar duk an sallamesu aiki.

"Gwamnan kamar yadda ya umarta, wannan sallamar bata shafi dukkan hukumomin da kundun tsarin mulkin kasar Najeriya ya tanadar ba a jihar.

"A saboda haka, dukkan kwamishinoni ana bukatar su muka lamurran ma'aikatunsu hannun manyan sakatarorinsu, banda ma'aikatan tsaron cikin gida wacce Rtd DIG Mohammed Ibrahim Tsafe ke shugabanta.

"Ana bukatar shugabannin hukumomi da su mika shugabancin hukumominsu ga manyan daraktoci. Shugaban ma'aikatan jihar zai cigaba da kula da ofishin sakataren gwamnatin jihar," takardar tace.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kone ofishin 'yan sanda, sun sheke mutum 13 a jihar Neja

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun halaka shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, reshen jihar Imo, Okiemute Mrere.

An kashe Mrere ne daren Asabar kan babban titin Owerri zuwa Fatakwal dake Owerri, The Punch ta gano hakan a ranar Litinin.

Babban jami'in hukumar ya tabbatar da hakan inda yace an ga gawar shugaban a daji da safiyar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel