Rundunar Yan Sanda Ta Gano Yan Bindigan da Suka Kashe Ahmed Gulak, Ta Sheƙe Wasu

Rundunar Yan Sanda Ta Gano Yan Bindigan da Suka Kashe Ahmed Gulak, Ta Sheƙe Wasu

- Rundunar yan sandan jihar Imo, ta bayyana cewa ta gano waɗanda suka kashe Ahmed Gulak

- Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abutu Yaro, shine ya bayyana haka a wani jawabi da rundunar ta fitar ɗauke da sa hannunsa

- Jami'ai sun kwato makamai da suka haɗa da bindigun AK-47, bindigar hannu da motocin da suka yi amfani da su wajen kisan

Kwamishinan yan sandan jihar Imo, Abutu Yaro, yace jami'an hukumar yan sanda sun gano waɗanda suka kashe Ahmed Gulak, fitaccen ɗan siya kuma jigo a APC, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa a Ibadan

Kwamishinan ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya aike wa hukumar dillancin labarai (NAN) ɗauke da sanya hannun sa ranar Lahadi.

Yace Jami'ai sun ɗauki matakin gaggawa bayan samun sahihin bayanai kan maharan, nan danan suka bi sawun su kuma suka gano su.

Rundunar Yan Sanda Ta Gano Yan Bindigan da Suka Kashe Ahmed Gulak, Ta Sheƙe Wasu
Rundunar Yan Sanda Ta Gano Yan Bindigan da Suka Kashe Ahmed Gulak, Ta Sheƙe Wasu Hoto: @thecableng

Jami'an sun gano cewa maharan mambobin ƙungiyar IPOB ne, a cewar kakakin yan sandan jihar, Bala Elkana.

Yace: "Bayan samun bayanan waɗanda suka aikata kisan, da motar da suka yi amfani da ita, mun kuma samu cikakken bayanin inda maharan suka bi bayan aikata kisan. Direban Gulak da wani mutum sun bamu cikakken bayani."

"Mun bi su zuwa garin Afor Enyiogugu ƙaramar hukumar Aboh-Mbaise, inda muka iske su suna raba wa mutanen ƙauyen albasar da suka yi fashinta daga wata motar Arewa."

KARANTA ANAN: Ahmed Gulak Ya Fita Masaukinsa Ba Tare da Sanin Mu Ba, Yan Sanda Sun Yi Ƙarin Haske

"Da suka hangi jami'ai na zuwa garesu, sai suka buɗe wuta, da yake jami'an na cikin shirin kota kwana sai suma suka maida martani, dukka mutum shida da suka kashe Gulak tare da wasu mutum huɗu yan tawagar su, mun ji musu munanan raunuka wasun su sun mutu."

Yan sandan sun ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku, ƙaramar bindiga fistol ɗaya, alburusai 92 da wani ƙullin kayan ta'addancin su, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan yace a yayin fafatawar jami'ai biyu sun samu raunin harbin bindiga amma sun tsira babu wanda ya rasa ransa.

Ya kuma yaba wa jami'an da suka gudanar da aikin, ya roƙe su su cigaba da baiwa al'umma tsaro yadda ya kamata.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa Tare da Wasu Mutum Uku

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da wani ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa a kan hanyarsa ta zuwa Jos.

Shugaban kwamitin hulɗa da jama'a na majalisar, Hon Mohammed Omadefu, shine ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel